Obaseki: Bayan kwamishanoninsa 3 sunyi murabus, jami'in yakin zabensa da wasu 2 sun koma APC

Obaseki: Bayan kwamishanoninsa 3 sunyi murabus, jami'in yakin zabensa da wasu 2 sun koma APC

- Abubuwa na neman dagulewa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki

- Ma'aikatansa da magoya bayansa na hannun riga da shi ana sauran yan makonni zaben gwamnan jihar

- Kawo yanzu mambobin kwamitin yakin neman zabensa akalla uku sun yi murabus kuma sun koma bayan dan takaran APC

Wani jami'in yakin neman zabe Godwin Obaseki a jihar Edo, Patrick Iyoha, ya yi murabus daga kwamitin tafiyar.

A cewar jaridar Daily Sun, wasu karin jami'an kwamitin yakin neman zaben biyu, Gabriel Oiboh da Osanyemwere Osawe, sun raba jaha da gwamnan, sun yi mubaya'a ga abokin hamayyarsa.

Yayinda Iyoha ya ajiye aikinsa a hukumar kula da tsaftar muhalli, Oiboh da Osawe sun ajiye aikinsu a hukumar makarantun firamaren jihar.

A wasikar murabus dinsa, Iyoha ya mika godiyarsa ga gwamnan bisa damar da ya bashi na yiwa jihar Edo aiki.

Shi kuma Oiboh a wasikar murabus dinsa, ya bayyana cewa rikice-rikice siyasan jihar da kokarinsa tilastashi sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC, zuwa Peoples Democratic Party, PDP, ya sa ya yanke shawarar ajiye aikin.

A yanzu, kimanin kansiloli 17 sun fita daga PDP kuma sun koma APC.

KU KARANTA: Allura ta tono garma: Matashi, Haruna Mohammed, ya yiwa kakarsa fyade

Obaseki: Bayan kwamishanoninsa 3 sunyi murabus, jami'in yakin zabensa da wasu 2 sun koma APC
Obaseki
Asali: UGC

A jiya, Kwamishanoni uku a hukumar cigabar yankuna masu arzikin mai da isakar gas na jihar Edo, sun yi murabus daga gwamnatin Godwin Obaseki, kuma sunyiwa abokin hamayyarsa, Osaze Ize-Iyamu, mubaya'a.

Rahoton TVC News ya bayyana cewa sun ajiye ayyukansu ne a yau Litnin, 27 ga watan Yuli, 2020.

Ga jerin sunayensu:

1) Hon Osamwonyi Atu

2) Hon Emmanuel Odigie,

3) Alhaji Rilwanu Oshiomhole

A bangare gudam tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole, ya tabbatarwa mabiya jam'iyyar cewa zasu samu gagarumin nasara a zaben bana.

Za'a gudanar da zaben ne ranar Asaba, 19 ga watan Satumba, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng