Kano: Dan takarar gwaman PRP a zaben 2019, Takai, ya koma APC
Dan takarar gwamna na jam'iyyar People’s Redemption Party, PRP, a zaben shekarar 2019 a jihar Kano, Malam Salihu Sagir Takai, ya koma jamiyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
Mai magana da yawun Takai, Abdullahi Musa Huguma ne tabbatar da komawarsa jam'iyyar ta APC kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Huguma ya ce ya koma jam'iyyar ta APC ne bayan tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki a kananan hukumomi 44 na jihar har ma da yan boko, malaman addini, da kwararru da suka tafiyar siyasa da shi tun 2011.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Na fi jin dadin yi wa mata da suka manyanta fyade - Mai laifi
Ku saurari karin bayani ...
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng