Badakalar da ta mamaye hukumar NDDC laifin gwamnatin da ta gabata ne - Lai Mohammed

Badakalar da ta mamaye hukumar NDDC laifin gwamnatin da ta gabata ne - Lai Mohammed

Ministan labarai da al'adu Alhaji Lai Mohammed, ya fayyace babban dalilin da ya sa yake ganin cewa shi ne musabbabin da ya haddasa badakalar rashawa a hukumar NDDC ta raya yankin Neja Delta.

Ministan ya ce rikon sakainar kashi da halin ko in kula da gwamnatin baya ta nuna a kan hukumar NDDC shi ya janyo badakala ta zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa hukumar.

Da ya ke zantawa da manema labarai a ranar Talata, Ministan ya ce tuhumce-tuhumce na rashawa da ke ci gaba da fitowa daga hukumar a baya-bayan nan ya sa ana yi wa gwamnatin yanzu mummunar fahimta.

Alhaji Mohammed ya ce badakalar rashawa da ta mamaye wasu hukumomi da ma'aikatun gwamnati, ya sa 'yan Najeriya da dama suna kalubalantar kokarin da gwamnatin yanzu take yi a kan yaki da rashawa.

Lai Mohammed
Hoto daga jaridar The Punch
Lai Mohammed Hoto daga jaridar The Punch
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar the Cable ta ruwaito, ministan ya ce da a ce gwamnatin baya ta yi abin da ya dace wajen sanya idanun lura a kan hukumar, da duk wannan hargitsi da ya mamaye ta a yanzu bai wakana ba.

Sai dai ministan ya kuma yi gargadi gami da mayar da martani ga 'yan adawa, inda ya ce idan akwai mai ganin gwamnatin yanzu ba ta dauki yaki da rashawa da muhimmanci ba, 'to ga mai fili kuma ga mai doki'.

Ministan ya ce idan akwai har akwai wadanda suke ganin isassu ne kuma za su yi ruf da ciki kan kudin gwamnati ba tare da sun fuskanci hukunci mai tsauri ba, 'to su ce kule su gani'.

Ya ce wasu ‘yan Najeriya na ta cece-kuce a kan zargin rashawa da ake yi wa wasu manyan cibiyoyin gwamnatin tarayya da suka hada da NDDC, NSITF da EFCC.

KARANTA KUMA: Ina jin dadin kasancewata shugaban kasa yayin da rayuwar 'yan Najeriya ta inganta - Buhari

Ya ce, “Wasu, musamman ‘yan adawa, suna fassara wannan ci gaban da alamun cewa gwamnatin ta yi sanyi a yaki da rashawa.

“A takaice, babban jam’iyyar adawa ta PDP ta yi amfani da wannan damar wurin kira ga shugaban kasa da ya yi murabus. Wannan kiran ba komai bane face bata baki.

“Bari in sake jaddadawa, yaki da rashawar gwamnatin nan yanzu aka fara. Tana nan daram babu gudu balle ja da baya.

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi suna nagari a duniya a kan yaki da rashawa. Zai ci gaba da wannan jagoranci. Babu wanda ya isa ya bata masa suna duk da a karkashin mulkin PDP din aka yashe kasar nan.

“Duk wanda bai aminta da wannan yaki da rashawar ta shi ba, ya gwada mu ya gani ko zai yi nasara.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel