COVID-19: Gwamnatin Osun ta haramta yin Sallar Idi amma ta amince ayi Sallar Juma'a

COVID-19: Gwamnatin Osun ta haramta yin Sallar Idi amma ta amince ayi Sallar Juma'a

Gwamnatin jihar ta soke Sallar Idi a fadin jihar a yayin da al'ummar Musulmi ke shirye shiryen gudanar da bukukuwan babbar Sallar wannan shekarar.

Sakataren gwamnatin jihar (SSG), Prince Wole Oyebamiji, ya tabbatar da cewar ba za a gudanar da Sallar Idi a jihar ba saboda annobar Coronavirus.

Ya ce, duba da kokarin jihar na ganin ta bi dukkanin matakan kariya daga yaduwar Coronavirus, kuma Sallar Idi da Juma'a sun fado a rana daya, wannan yasa aka soke Sallar Idin.

SSG ya ce a yanzu al'umar Musulmi zasu gudanar da Sallar Juma'a ne kawai, nan ma sai anbi matakan kariya da aka shar'anta na hana yaduwar cutar.

Ya yi nuni da cewa jihar har yanzu tana fuskantar karuwar masu kamuwa da cutar COVID-19 a kowacce rana, wanda hakan ba abun da za ayi wasa da shi bane.

Oyebamiji ya nuna damuwarsa kan cewar mutane da dama, wadanda ba a san lafiyarsu ba, zasu shigo cikin jihar domin gudanar da bukukuwan Sallah.

Ya ce jihar Osun ba zata iya lamuncewa da wani babban taron jama'a ba kamar yadda za a samu a filayen Sallar Idi, wanda dole a samu karya dokokin kariya daga cutar COVID-19.

"Shuwagabanninmu ta fuskar kiwon lafiya sun nuna damuwarsu kan yawaitar masu dauke da cutar Coronavirus a jihar, wanda kuma sakamakon rashin bin dokokin da aka gindaya ne.

"Gwamnatin jihar ba za ta so al'ummarta su ci gaba da kamuwa da wannan cuta mai hatsari ba, musamman ga tsofaffi ko masu fama da rashin lafiya.

"Gwamnatin jihar Osun ba zata yi kasa a guiwa wajen yaki da yaduwar Coronavirus ba, da nufin kawar da ita daga jihar kwata kwata.

"Gwamnatin jihar, za ta ci gaba da daukar matakai na kare al'ummar jihar da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar jama'a."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel