Sabon Sauya sheka: Yakubu Dogara ya kwashi dimbin yan majalisar PDP zuwa gidan Mai Mala Buni

Sabon Sauya sheka: Yakubu Dogara ya kwashi dimbin yan majalisar PDP zuwa gidan Mai Mala Buni

Kimanin kwanaki hudu bayan sauya sheka, tsohon Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, a ranar Litnin ya jagoranci wasu mambobin majalisa zuwa gidan gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni.

Tawagar sun gana da Buni, wanda shine shugaban kwamitin rikon kwaryan All Progressives Congress (APC), don tattaunawa kan yiwuwan sauya shekansu.

Buni, wanda ya karbi bakuncinsu a gidansa dake Abuja, ya ce kofar APC bude take ga duk wadanda ke da tunani irin na cigaba.

Sun yi ganawar ne a sirrance tsakanin karfe 1 da 2 na rana.

Yan majalisan da Yakubu Dogara ya jagoranta zuwa gidan Buni sune Danjuma Usman Shidda (APGA, jihar Taraba), Sam Izuigbo (Anambra); Hembe Hembe (Benue) da wani tsohon dan majalisar dokokin jihar Bauchi, Alhaji Saidu.

Sabon Sauya sheka: Yakubu Dogara ya kwashi dimbin yan majalisar PDP zuwa gidan Mai Mala Buni
Sabon Sauya sheka: Yakubu Dogara
Asali: Twitter

Majiyar da aka sakayewa suna tace: "Dogara ya yi tattaunawa sosai da su kan sauya shekar wasu mambobin majalisar wakilai daga wasu jam'iyyu zuwa APC."

"Akwai alamun da aka gane a ganawar cewa wasu manyan yan majalisar dokokin tarayya daga jihar Bauchi zasu hadu da Dogara a APC ba da dadewa ba. Tattaunawar Litinin ya tattari yiwuwan sauye sheka daga PDP zuwa APC."

"Shugaban APC ya ce jam'iyyar ba ta daura wasu sharruda ga masu sauya sheka."

An samu labarin cewa bayan tattaunawar, Buni da tawagar yan majalisan sun tafi wani gida dake unguwar Wuse 2 domin ganawa da wasu kuma.

KU KARANTA: Shin da gaske ne rago ya kamu da coronavirus a Arewacin Nigeria?

A bangare guda, Hon. Aminu Tukur, na hannun daman Rt. Hon. Yakubu Dogara, ya jaddada aniyarsu na yiwa gwamnan Bauchi Sanata Bala Abdulkadir ritaya a siyasa kamar yadda suka yiwa tsohon gwamnan jihar M.A Abubakar.

Hon. Aminu Tukur ya ce, suna fatan jam'iyyar APC ta ba Dogara tikitin takarar shugabancin kasar a 2023. Ya kuma ce yunkurin wasu 'yan PDP na yiwa Dogara kiranye ba zai yi nasara ba.

Wannan na zuwa ne, bayan da Dogara ya canja sheka daga jam'iyyar PDP ya koma APC. Lamarin da ya jawo cece kuce tsakanin jam'iyyun biyu daga matakin kasa zuwa matakin jiha.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel