FG ta ce ranakun Alhamis da Juma'a ne hutun Babbar Sallah na 2020

FG ta ce ranakun Alhamis da Juma'a ne hutun Babbar Sallah na 2020

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Alhamis 30 ga watan Yuli da Juma'a 31 ga watan Yulin shekarar 2020 a matsayin ranakun hutu domin bikin Babbar Salla wato Eid-el-Kabir na wannan shekarar.

Hakan na cikin wata sanarwa ce da sakataren dindindin na Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, Georgina Ehuriah ta fitar a ranar Talata 28 ga watan Yuli.

A cewar sanarwar, Ministan Ma'aikatar Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya taya al'ummar musulmi da sauran yan Najeriya da ke gida da kasashen waje murnar bikin ta Babbar Sallah.

Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranakun hutun Babbar Sallah na 2020
Rauf Aregbesola
Asali: Facebook

"Ya yi kira ga musulmi su cigaba da yada kauna, zaman lafiya, karamci da sadaukar da kai kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar kuma suyi amfani da lokacin domin yin adduo'in zaman lafiya, hadin kai da cigaba musamman a yanzu da kasar ke fama da annobar korona," a cewar wani sashi na sanarwar.

DUBA WANNAN: Na fi jin dadin yi wa mata da suka manyanta fyade - Mai laifi

Ministan ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya su bawa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari goyon baya a yayin da ta ke kokarin yaki da annobar ta COVID-19.

Ya kuma ce Gwamnatin Tarayya za ta cigaba da kokarin wanzar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al'umma domin ganin kasar ta cimma manufofin da ta saka a gaba.

Aregbesola ya kuma shawarci yan Najeriya su rika daukan matakin kare kansu daga kamuwa daga cutar COVID-19 ta hanyoyin bayar da tazara, tsaftace jikinsu da sauran hanyoyin da hukumomin lafiya suka sanar.

A baya Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Sarkin Musulimi Sa'ad Abubakar ya bukaci hakimai da shugabannin addini suyi limancin sallar Idi a masallatan Juma'a a maimakon zuwa filayen sallar Idi.

Sultan din ya bayar da wannan shawarar ce yayin da ya ke sanar da cewa a ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2020 ce ranar babbar Sallah kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

A cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba 22 ga watan Yuli, Sultan Abubakar ya yi kira ga alummar musulmi suyi adduo'in zaman lafiya da samun cigaba a kasar.

"Mai alfarma, Alhaji Muhammad Saad Abubakar CFR, mni, Sultan din Sokoto kuma shugaban Kwamitin Koli ta Musulunci ta Najeriya, NSCIA, ya sanar da cewa ranar Juma'a 31 ga watan Yulin 2020 da ya yi daidai da ranar 10 ga watan Zulhijja ta 1441 AH ne za ayi babbar sallar wannan shekarar," in ji sanarwar.

"Bugu da kari, duba da halin da ake ciki na annobar Covid 19, Sultan yana shawartar dukkan hakimai da Limamai a jihar Sokoto suyi sallar Idi a masallatan Juma'a da ke garuruwansu da maimakon filayen Idi.

"Kazalika, Majalisar Kolin tana shawartar sauran musulmi a dukkan sassan kasar suyi sallar Idi a masallatan Juma'a domin taimakawa wurin dakile yaduwar annobar Covid 19."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel