Amfani da magunguna 5 na gwanda ga lafiyar jikin dan Adam

Amfani da magunguna 5 na gwanda ga lafiyar jikin dan Adam

Ba haka kawai bane Ubangiji ke yin kayan marmari, tabbas akwai wasu manyan baiwa da ke tattare da su. Gwanda babban abun marmari ne mai tarin albarkatu.

Gudumawar da gwanda ke bai wa lafiyar jikin dan Adam na da tarin yawa. Tana dauke da sinadaran magani sanannu da jama'a da yawa a fadin duniya suka sani.

Ilimi ya nuna cewa gwanda tana dauke da sinadaran Vitamin A, C, E da K.

Tana kunshe da Magnesium, potassium, niacin, carotene, protein, fiber da kuma papain, wanda ke maganin mura da kashe wasu kwayoyin cuta a jiki.

Za ka sha matukar mamaki idan ka gano amfanin gwanda.

Abin mamakin shine, bincike ya nuna cewa hatta 'ya'yanta na matukar taimakawa fatar dan Adam tare da sanyata walkiya.

Ga wasu amfanin gwanda 5 ga dan Adam.

1. Tana kara hasken fata

Sanannen abu ne cewa gwanda tana goge fata tare da taimakawa wurin cire dattinta. Kunsar sinadarin Vitamin C da tayi yasa take bada kariya wurin lalacewar fata.

2. Tana hana bayyanar alamun tsufa ko shekaru

Gwanda tana saka fata ta yi laushi da santsi. Tana iya bada wannan amfanin ne sakamakon sinadaran Vitamin da ke cikinta.

Akwai sinadarin alpha hydroxy acid wanda ke hana bayyanar alamun shekaru ta hanyar kashe matattun 'ya'yan halitta. Vitamin C da E suna boye shekaru tare da rage tsufa.

3. Tana yakar fimfus da tabbansu

Bincike ya nuna cewa sinadarin Papain da ke kunshe a gwanda na goge fata. Hakan yasa kofofin fata da suke toshe ke budewa.

Hakazalika, matacciyar fata na fita da taimakon sinadarin hydroxy acid. Hakan na hana fimfus da tabbai.

Amfani da magunguna 5 na gwanda ga lafiyar jikin dan Adam
Amfani da magunguna 5 na gwanda ga lafiyar jikin dan Adam. Hoto daga Pulse.ng
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Yadda matashi ya shiga sata amma ya kare da yi wa tsohuwa fyade

4. Gwanda tana hana bushewar fata

A nan, 'ya'yan gwanda na bada mamaki. Ana amfani da su ga fata mai laushi ko mai tauri.

Sakamakon sinadaran Vitamin da Minerals da ta kunsa, tana hana bushewar fatar mai amfani da ita.

5. Gwanda na maganin tattarewar fata sakamakon tsufa da kuma tsagewar kafa yayin sanyi

Bincike ya nuna cewa gwanda na hana bayyanar tattarewar fata sakamakon tsufa sannan tana maganin tsagewar kafa yayin sanyi.

Tun a farko an san tana kunshe da sinadaran Vitamin C, wannan kadai yana iya yakar duk wani abu da ke lalata fata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel