Gwamnatin tarayya ta warewa 'yan siyasa kashi 10% na guraben kananan ma'aikata 774,000 da za ta dauka

Gwamnatin tarayya ta warewa 'yan siyasa kashi 10% na guraben kananan ma'aikata 774,000 da za ta dauka

Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta ware wa 'yan siyasa kashi 10 cikin dari na kananan ma'aikata 774,000 da za ta dauka.

Gwamnatin ta kasafta kashi 10 cikin dari na guraben ayyuka 774,000 ga ‘yan siyasa, in ji mai magana da yawun kwamitin da zai jagoranci ragamar daukan aikin na jihar Kano, Abubakar Muhammad-Janaral.

Yayin zantawa da manema labarai na jaridar Premium Times a ranar Litinin, Muhammad-Janaral ya ce tuni an rarrabawa 'yan siyasa takardu 4,400 na neman aikin daga cikin gurabe 44,000 da aka tanadar wa jihar Kano.

Jami'i a kwamitin shirin ayyuka na musamman ya ce hakan ya faru ne domin bin umarnin da gwamnatin tarayya ta shata na bai wa 'yan siyasa kashi 10 na guraben aikin.

Muhammad Janaral ya ce makasudin yin hakan shi ne magance kutse da hawan kawara da 'yan siyasar za su yi a shirin na daukan matasan aiki.

'Yan kwamitin da za su jagoranci ragamar daukan matasa 44,000 aiki a jihar Kano
'Yan kwamitin da za su jagoranci ragamar daukan matasa 44,000 aiki a jihar Kano
Asali: Twitter

Ya ce: "Mun fara rarraba kashi 10 cikin 100 na guraben ayyukan 44,000 ga 'yan siyasa saboda ba ma son tsangwama a yayin sauke nauyin da gwamnatin tarayya ta rataya mana."

"Wadannan 'yan siyasa sun hadar da gwamna, mataimakinsa, sanatoci, 'yan majalisar wakilai, 'yan majalisar dokokin jiha, shugabannin kananan hukumomi, da kansiloli."

Ya ci gaba da cewa, wannan tsarin guda daya ne a duk fadin kasar kamar yadda gwamnatin tarayya ta umarci dukkanin kwamitocin jihohin da su rarraba kashi 10 cikin 100 ga 'yan siyasa.

Ya na cewa kwamitin na jihar Kano ya kuma kafa wani kwamitin a kowace karamar hukumar da ya kunshi sarakunan gargajiya, malamai da kuma limamai da za su sa ido a kan shirin na daukan aiki.

KARANTA KUMA: Buhari ya naɗa mataimakan kwamishina 2 a hukumar NAICOM

A cewarsa, kwamitin zai fara rarraba takardun neman daukan aikin ga matasa marasa abun yi kuma suka nuna bukatar samun gurbi a shirin, inda daga bisani za'a tantance wadanda suka fi cancanta.

Legit.ng ta fahimci cewa, aikin dai za’a dauki matasa 1000 ne daga kowace karamar hukuma 774 dake fadin Najeriya.

A yayin da jihar Kano ta ke dauke da kananan hukumomi 44, tana da gurabe 44,000 kenan.

Za a rika biyan matasan N20,000 a kowane wata har na tsawon watanni uku domin rage radadin zaman kashe wando musamman a yankunan karkara.

Matasan da za a dauka za su rika sharar titi, tsaftace magudanan ruwa, bayar da hannu domin rage cunkoson motoci a kan titi da sauran ayyuka na ci da karfi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel