Duk da barazanar Kwankwasiyya, sai mun ciyo bashin N340bn - Gwamnatin Ganduje

Duk da barazanar Kwankwasiyya, sai mun ciyo bashin N340bn - Gwamnatin Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa babu ja da baya wajen niyyar karban bashi don gina layin dogon jirgin kasa a cikin garin Kano, wanda aka yanke bayan neman shawari daga masu ruwa da tsaki a jihar.

Gwamnatin jihar ta jaddada cewa an shirya ginin layin dogon ne domin fadada harkokin kasuwanci a jihar da saukake sufuri don amfanin gona a jihar.

ThisDay ta ruwaito cewa kwamishanan labaran jihar, Muhammad Garba, ya saki takarda a daren Litnin domin martani ga Kwankwasiyya kan aikin.

Ya ce babu irin sukan da zai hana gwamnatin jihar aiwatar da manyan ayyuka don mayar da jihar Kano babbar birni.

Garba ya ce tun da bankin shiga da ficen kasar China ya amince da baiwa jihar bashin, gwamnatin jihar ba zata bata lokaci ba wajen kaddamar da ginin da za'a fara daga kasuwan kayan hatsi dake Dawanau zuwa Bata.

Ya ce an bi dukkan ka'idojin da ya kamata, wanda ya hada da sa hannun majalisar dokokin jihar, majalisar dokokin tarayya da wasu manyan ma'aikatun gwamnatin tarayya.

Duk da barazanar Kwankwasiyya, sai mun ciyo bashin N340bn - Gwamnatin Ganduje
Gwamnatin Ganduje
Asali: UGC

KU KARANTA: Yadda ma'aikatar lafiya, NCDC, FRSC, NPHCDA suka bannatar da 1.7bn da sunan Coronavirus

A jiya Legit ta kawo muku rahoton cewa Babbar darikar siyasar nan ta Kwankwasiyya, ta maka gwamnan jihar Kano a kotu dangane da shirinsa na karbo rancen Yuro 684,100,100 daga wani babban banki na kasar China.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kulla aniyyar karbo bashi wannan kudi da sun kai kimanin Naira biliyan daga kasar China, domin aiwatar da aikin shimfida layin dogo mafi gudu a jihar Kano.

A dalilin haka darikar Kwankwasiya ta yi wani dogon rubutu na korafi da kalubalantar wannan yunkuri da gwamna Ganduje ke shirin yi, wanda a cewarta ba a biyo da shi ta hanyar da ta dace ba kuma ya sabawa ka'ida.

Kwankwasiyya ta rubuta takardar mai dauke da korafi tare da kalubalantar gwamnatin jihar Kano da kuma majalisar dokoki ta jihar kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Haka kuma wasikar tana jan hankalin ofishin jakadancin China a Najeriya, Ofishin kula da bashi na fadar shugaban kasa da kuma Bankin Raya kasar China wanda gwamnan ke shirin karbo rancen a wurinsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel