Shin da gaske ne rago ya kamu da coronavirus a Arewacin Nigeria?

Shin da gaske ne rago ya kamu da coronavirus a Arewacin Nigeria?

Wani labari da aka wallafa a kafar sada zumuntar facebook na nuni da cewa wani rago ya kamu da cutar nan mai toshe numfashi watau coronavirus a jihar Niger, a ranar 12 ga watan yulin 2020.

Bayanin ya nuna hoton rago da kafafuwa a daure an saka mashi ruwa.

Jihar Niger tana yankin arewa ta tsakiya ne a Nigeria.

A wasu bayanai daban da aka wallafa, masu da'awar hakan sun bayyana cewa ragon ya kasance a Katsina da Kano, cikin jihohin arewacin Nigeria.

Labarin ya bazu a kafar sada zumuntar facebook fiye da sau dari. Da yawan yan Nigeria sun ruwaito labarin amma basu bada kwararriyar hujja ba akan hakan.

Anya hoton na nuni da cewa ragon ya kamu da cutar korona kuwa, kuma a ina aka dauki hoton?

Shin da gaske ne rago ya kamu da coronavirus a Arewacin Nigeria?
Shin da gaske ne rago ya kamu da coronavirus a Arewacin Nigeria?
Asali: Facebook

KU KARANTA: Buhari ya shiga ganawa da gwamnonin jam'iyyar APC

Babu wata fitacciyar kafar labarai da ta ruwaito cewa ragon ya kamu da cutar korona.

Bamu samu kwakkwarar hujja akan hoton ba. Duk wani bincike akan hoton na nuni da abu daya ne.

An wallafa hoton a kundun hotuna 28 na ban dariya da barkwanci a kafar watsa labarai na Opera a ranar 15 ga watan yulin 2020. Hoton kuma an wallafa shi ga masu san nishadi, amma bamu samu wani karin bayani akan gaskiyar abinda yake ta yaduwa a kafar sada zumuntar zamani ba.

Shugaban kungiyar yan jarida na jihar Kano, Nasir Yusuf ya musanta hakan ga Africa Check.

"Akwai yan jarida da yawa a Kano kuma cikinmu babu wanda ya wallafa labarin na cewa rago ya kamu da coronavirus. Wannan shine karon farko dana fara jin hakan," A cewar Yusuf.

Ya kara da cewa bai taba jin hakan daga daya daga cikin yan jaridar Niger ko Katsina ba.

Kungiyar takaita yaduwar cututtuka ta Nigeria (NCDC) ta bayyana mana cewa ba dabbar da aka yiwa gwajin cutar korona a kasar. Ba wani dakin gwaji da ya bayyana cewa rago ya kamu da cutar korona.

A cewar kungiyar kiwon lafiya na kasa (WHO), "yawancin karnuka da mazurai da suke rayuwa tare da mutane masu dauke da cutar sun kamu".

WHO tana shawartar mutanen da suka kamu da cutar dasu nisanta kansu daga dabbobi. Amma a yanzu babu wani ingantaccen rahoton da yayi nuni akan rago ya kamu da cutar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel