Yadda ma'aikatar lafiya, NCDC, FRSC, NPHCDA suka bannatar da 1.7bn da sunan Coronavirus

Yadda ma'aikatar lafiya, NCDC, FRSC, NPHCDA suka bannatar da 1.7bn da sunan Coronavirus

Ma'aikatar lafiya, hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC, hukumar kiyaye hadura kan hanyoyin Najeriya FRSC, da wasu hukumomin gwamnatin Najeriya sun yi almubazzarancin makudan kudin al'umma da sunan yaki da Coronavirus.

Bayanai da Dataphyte ta samu daga shafin bayyana baitul mali (OTP) tsakanin 1 ga watan Maris zuwa 27 ga Yuni, 2020 ya nuna abubuwa 84 da ma'aikatun gwamnatin Najeriya suka saya domin yaki da COVID-19.

Ma'aikatun sun hada da hukumar cigaban kananan asibitoci a Najeriya (NPHCDA), hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC, hukumar kiyaye hadura kan hanyoyin Najeriya FRSC, Ma'aikatar lafiya da hukumar sibil defens (NSCDC)

Daga ciki, Hukumar ta yi ikirarin siyan sinadarin tsaface hannu (500ml) farashin N5,600 ga kowani daya na kimanin milyan N5.6.

Austin Chimeze, mammalakin daya daga cikin manyan shagunan sayar da magunguna a Legas ya yi mamakin yadda za'a ce an sayi sinadarin tsaftace hannu 500ml a farashin N5600.

A cewarsa, "Ko a lokacin da Korona tayi tsauri, farashin 500ml na sinadarin tsaftace hannu N3000 ne. Muna sayar da kwalinsa N12,000 kuma guda 12 ke cikin."

Wani dan kasuwan sayar da magunguna a shagon maganin Rita dake Lekki, Lagos, Olusola Olarinto, ya ce babu wanda zai sayi sinadarin tsaftace hannu da akayi a Najeriya a farashin nan, musamman 500ml.

A cewar shafin, ma'aikatun gwamnatin sun bannatar da N1.69 billion kan Korona a watanni uku.

Yadda ma'aikatar lafiya, NCDC, FRSC, NPHCDA suka bannatar da 1.7bn da sunan Coronavirus
Yadda ma'aikatar lafiya, NCDC, FRSC, NPHCDA suka bannatar da 1.7bn da sunan Coronavirus
Asali: UGC

Lissafi:

Binciken Dataphyte ya nuna cewa hukumar NPHCDA ta kashe N1.36bn . Kashi 80% na kudin da sauran ma'aikatun suka kashe cikin watanni uku.

Yayinda hukunar NCDC ta kashe ₦42.16 million, NSCDC ta kashe ₦170.7 million, ma'aikatar lafiya ta kashe ₦86.63 million, kuma FRSC spent ₦32.26 million.

Binciken Dataphyte ya nuna cewa ba'a katabta yawancin saye-sayen ba kuma an yi rufa-rufa cikin wasu. Wasu abubuwan da lura an bada kwangilan sayen kayayyaki a farashin da ko a kasuwa sun fi haka.

Misali, hukumar NPHCDA ta kashe ₦39.3 million kan amawali amma ba'a ambaci adadin amawalin da aka saya ba.

Duk yunkurin da akayi na jin ta bakin hukumar NPCHCDA ya ci tura.

Ba a hukumar NPHCDA kadai abin ya kare ba, ma'aikatar lafiya ta biya wasu mutane N15 million da N71 million ba tare da bayyana dalilin ba.

A hedkwatar hukumar NSCDC kuwa, an biya N35.3million na sayan amawali, N15 million na sayan sabulun wanke hannu.

Duka a ma'aikata daya kuma, an baiwa wani dan kwangila N26.26 million kudin kawo sabulun hannu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel