Bidiyo: Yadda Gwamnan PDP ya sha 'ihu barawo' daga jama'arsa

Bidiyo: Yadda Gwamnan PDP ya sha 'ihu barawo' daga jama'arsa

Gwamnan jihar Edo, Gwamna Godwin Obaseki ya sha ihun 'barawo, bama yi' daga wurin jama'ar jiharsa a yau Lahadi.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, Obaseki ya kai wa babban basaraken jiharsa ziyara ne har fadarsa.

Amma kuma cincirindon jama'ar da ya kamata su karbesa da hannu bibbiyu tare da jinjinawa gwamnan nasu, sai suka dinga kida tare da kiransa da barawo.

A bidiyon, an ji muryoyi tare da ganin hotunan jama'a suna kida tare da kiran sunansa suna kiransa da barawo.

An ji muryoyin na cewa, "Obaseki Ole, Ole, Ole. Obaseki Ole. PDP Ole, Ole, Ole. PDP Ole."

A harshen hausa hakan na nufin, "Obaseki barawo, barawo, barawo. Obaseki barawo. PDP barawao, barawo, barawo, PDP barawo."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel