Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 16 a Abuja da Neja

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 16 a Abuja da Neja

Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutum shida yayin da ake nemi mutane biyar aka rasa a ranar Asabar biyo bayan saukar wani ruwan sama na mamako a garin Suleja na jihar Neja.

Jaridar Leadership ta ba da rahoton cewa ruwan saman da ya sauka tamkar da bakin kwarya da sanyin safiya ya haifar da ambaliyar ruwa a mafi akasarin yankunan garin Suleja.

Darakta Janar na Hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Neja, Ibrahim Ahmed Inga, shi ne ya ba da tabbacin hakan da cewa an tsinto gawawwaki mutum shida da ruwa ya tafi da su.

Yayin tattaro wannan rahoto, ya ce an nemi mutane 11 an rasa, amma yayin da aka tsamo gawar mutum shida, a yanzu mutum biyar ne kawai ba a san halin da suke ciki ba walau a raye ko a mace.

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 16 a Abuja da Neja
Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 16 a Abuja da Neja
Asali: Twitter

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 16 a Abuja da Neja
Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 16 a Abuja da Neja
Asali: Twitter

Ya ba da tabbacin cewa, ambaliyar ruwan ta fi muni a wasu yankuna biyu na jihar da suka hadar da; Unguwar Gwari da POP.

Haka zalika wata mata mai dauke da juna biyu tare da 'ya;yanta hudu, na cikin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da ta auku a yankin Gwagwalada da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, matar 'yar shekaru 27 mai suna Habiba Hamid, ta riga mu gidan gaskiya tare da 'ya'yanta; Ladifa, Rahama, Abdullatif da kuma Rabi'u.

An tafka ruwan sama na mamako da ya fara sauka tun da misalin karfe 2.00 na ranar Juma'a da daddare wanda ya ci gidaje da dama da suka datsi magudanan ruwa a unguwar mayanka da ke garin Gwagwalada ta birnin Abuja.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, masarautar Katsina ta kwaikwayi jihar Kano inda ta yanke hukuncin soke dukkan shagulgulan babbar sallah.

KARANTA KUMA: An kama ɗan Fasto da wasu mutum 5 da ake zargi da yi wa 'yar shekara 12 fyaɗe

Wannan na kunshe ne a wata wasika da masarautar ta tura ga sakataren gwamnatin jihar da kuma sa hannun sakataren masarautar Katsina, Mamman Ifo.

A shagalin duk babbar sallah, akwai fitaccen hawan nan da ake kira hawan bariki wanda sarki ke ziyartar fadar gwamnan jihar tare da hawan Durbar mai kayatarwa.

Kamar yadda wasikar ta ce, an soke shagulgulan sallar ne saboda hauhawar rashin tsaro da kuma annobar korona da ta addabi jihar.

Amma kuma, masarautar yayin da take taya daukacin Musulmi murna, ta yi kira garesu da su tsananta addu'a a kan Allah ya kawo zaman lafiya a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng