Zulum ya kai ziyara Damasak, ya bai wa gidaje 674 tallafi tare da duba aikin gidaje 1,000
‘Yan gudun hijira 674 da suka dawo gida a garin Damasak sun samu tallafin kayayyakin abinci da kudi daga wurin gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum a ranar Asabar yayin da ya kai musu ziyara har Damasak, babban birnin karamar hukumar Mobar ta jihar.
Jama’ar da suka dawo Damasak din ‘yan gudun hijar ne daga jamhuriyar Nijar. Sun tsere ne sakamakon harin mayakan ta’addanci na Boko Haram.

Asali: Twitter
Zulum ya duba yadda ake raba hatsi da kayayyakin hadin abinci ga kowanne gida. Bugu da kari, ya bada umarnin rarraba N10,000 ga kowanne gida don ko ta kwana.
Gwamnan ya samu rakiyar kwamishinan ayyuka da gyara na jihar, yayin da suka gangara don duba ginin gidaje 1,000 da ake yi don wadanda suka dawo daga gudun hijirar su samu matsuguni.

Asali: Twitter
Zulum ya bada umarnin fadada wurin aikin don samun damar karin gina gidaje ga ‘yan gudun hijirar da suka dawo gida. Zulum ya jinjina wa inganci da kuma yadda aikin ke tafiya.
Baya ga al’amuran walwala da jin kai da ya duba, gwamnan ya duba wurin noman rani da mazauna garin suka bari saboda mayakan Boko Haram da suka addabesu.
KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan ta'adda 47 sun mika wuya ga jami'an tsaro hadin guiwa
Bayan duba wurin, gwamnan ya bai wa ma’aikatar gyara umarnin gayyatar injiniyoyi don su duba yuwuwar gyara dukkan na’urorin ta yadda manoma za su iya amfana.
Baya ga harkar noma, Gwamna Zulum ya umarci masu aikin gyaran titi da su duba yanayin gadar Kam Kura da ta hada Najeriya da jamhuriyar Nijar.

Asali: Twitter
Kafin komawarsa Maiduguri a ranar, Zulum ya ziyarci babban asibitin Damasak da kuma hukumar soji da ke garin.
Gwamnan ya jinjinawa kokarin zakakuran dakarun sojin wurin bada kariya ga rayuka da kadarorin jama’a da ke garin.

Asali: Twitter
Ya yi kira ga kwamandan sojin da ya duba yuwuwar komawar manoma gona da wuri ba kamar yadda suke zuwa ba da karfe 10 na safe.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng