‘Yan sanda sun tarwatsa taron ‘yan Shi’a a garin Kaduna

‘Yan sanda sun tarwatsa taron ‘yan Shi’a a garin Kaduna

Rahotanni daga jaridar The Nation sun tabbatar da cewa, an sake yin karon batta tsakanin jami'an tsaro na 'yan sanda da kuma 'yan kungiyar IMN ta mazhabar shi'a a jihar Kaduna.

Mun samu cewa, jami'an 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna, sun tarwatsa taron mambobin kungiyar IMN wadda aka fi sani da shi'a a garin Zazzau.

An tarwatsa taron 'yan shi'ar ne yayin da suka bikin tunawa da shekaru shida bayan mutuwar 'ya'ya uku na shugaban IMN, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da wasu mabiyansa 32.

A yayin da mabiya mazhabar shi'a ke tsaka da wannan biki a makabartar Unguwar Bishar da ke cikin garin Zaria, motoci 6 na 'yan sanda dauke da makamai suka afkawa taron a sukwane.

Wannan lamari ya sanya 'yan shi'a suka fara kabarbari na Allahu Akbar, wato Allah da Girma ya ke, a yayin da jami'a tsaron suka yi musu tarnaƙi da barkonon tsohuwa.

‘Yan sanda sun tarwatsa taron ‘yan Shi’a a garin Kaduna
‘Yan sanda sun tarwatsa taron ‘yan Shi’a a garin Kaduna
Asali: Twitter

Sai dai shugaban gidauniyar Shuhada ta Kungiyar IMN reshen Zaria, Sheikh Abdulhamid Bello, ya ce sun saba gudanar da wannan biki duk shekara ta hanyar gudanar da addu'o'i da kai ziyara kaburburan wadanda suka gabace mu.

Sheikh Bello ya ce makasudin wannan biki shi ne tunawa da mabobobinsu da suka riga mu gidan gaskiya. "Ba ma son mu manta da mambobin wadanda suka mutu a mummunan lamarin da ya faru a ranar 25 ga watan Yulin 2014."

KARANTA KUMA: Ainihin dalilin da ya sa aka hana 'yan Najeriya samun aiki a Dubai

"A baya mun yi mufin gudanar da taron a Darur-Rahma, da ke Unguwar Dembo a kan hanyar Jos, inda aka binne mamatan, amma mun samu rahoton cewa 'yan sanda sun yi wa wurin shinge."

Ana iya tuna cewa, rikicin ranar Qudus a Zariya wani al'amari ne da ya faru tsakanin dakarun soji da mabiya shi'a a ranar 25 ga Yuli 2014, inda da dama suka rasa rayukansu ciki har da 'ya'yan Zakzaky guda uku.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel