Kano: Matashi ya soka wa kansa wuka har lahira saboda budurwarsa za ta auri wani

Kano: Matashi ya soka wa kansa wuka har lahira saboda budurwarsa za ta auri wani

Matashi mai shekaru 25 dan asalin jihar Kano mai suna Ashiru Musa Danrimi, ya kashe kansa ta hanyar sokawa cikinsa wuka a jihar Kano.

An gano cewa matashin ya aikata hakan ne bayan budurwarsa da suka zuba soyayya za ta aura wani mutum da ba shi ba.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, mamacin dan asalin gundumar Kadawa ne da ke karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano.

Hankalinsa ya tashi kuma ya yi matukar harzuka bayan da ya gano cewa budurwasa mai suna Ummi Muhammad ta yanke hukuncin auran wani mutum daban.

Bincike ya nuna cewa, ya mayar da hankali ba kadan ba a kan soyayyarsu saboda ya sadaukar da kudinsa, aljihunsa da lokacinsa.

An zargi cewa ya soka wa kansa wuka bayan samun wannan labarin.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sanda jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce 'yan sanda sun gaggauta mika shi asibitin kwararru na Murtala da ke Kano inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Habu Sani, ya umarci sake bincike mai tsanani kuma gamsasshe a kan mummunan lamarin.

Makwabtan mamacin sun bayyana alhininsu da mamaki a kan aukuwar lamarin, domin kuwa sun san irin soyayyar da ke tsakanin masoyan. Basu taba tsammanin za ta kare a hakan ba.

Kano: Matashi ya soka wa kansa wuka har lahira saboda budurwarsa za ta auri wani
Kano: Matashi ya soka wa kansa wuka har lahira saboda budurwarsa za ta auri wani. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan ta'adda 47 sun mika wuya ga jami'an tsaro hadin guiwa

A wani labari na daban, Wasu ma'aurata a kasar New Zealand daga yankin Chesterfield, Derbyshire sun yi nasarar wata gwagwarmaya a kotu inda aka amince da su saka wa dan su mai watanni hudu da haihuwa suna "Iblis" bayan an so hana su sanya wa dan wannan sunan.

Dan, wanda yake aiki a wani kamfani ya kai kokensa a kan cewa an wulakanta su shi da matarsa bayan suka je yi wa dan nasa da suka haifa yayin kulle rijista.

Ya ce, "muna jin dadin za mu je yi mishi rijista amma da muka isa sai matar ta kalle mu a wulakance.

"Ta ce ba zai taba samun aiki ba kuma malamai ba zasu koyar da shi ba. Na yi kokarin yi mata bayanin cewa bamu da addini kuma sunan a Girka yana nufin "mai kawo haske ko kuma safiya" amma ta ki saurarar mu.

"Ta ce shari'ar New Zealand bata aminta a sakawa da wannan sunan ba. Saidai mu je mu sauya mishi suna ko a gida mu dinga kiran shi da Iblis."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel