Ameachi ya umurci a fara jigilar fasinjojin jirgin kasar Kaduna-Abuja kafin Babbar Sallah
- Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi ya bayar da umurnin a fara jigilar fasinjojin jirgin kasar Kaduna-Abuja kafin Babbar Sallah
- Ministan ya bayar da wannan umurnin ne a yau Asabar ta shafin Twitter na Maaikatar Sufuri ta Tarayya
- Ameachi ya kuma umurci hukumar kula da jiragen kasar ta samar da hanyoyin dakile yaduwar korona kafin fara jigilar
Rotimi Amaeachi, ministan sufuri na Najeriya ya umurci Hukumar Jiragen Kasa,NRC, ta fara jigilar fasinjoji daga Kaduna zuwa Abuja kafin Babbar Sallar.
Za a gudanar da Babbar Sallar ne dai a ranar 31 ga watan Yulin shekarar 22 kamar yadda Sarkin Musulmi Saad Abubakar ya sanar.

Asali: Twitter
Ministan ya bayar da wannan sanarwar ce a shafin Twitter ta Maaikatar Sufuri a ranar Asabar 25 ga watan Yuli.
DUBA WANNAN: Kano: An ƙwace kujerar ɗan majalisar APC an bawa PDP
Ya kuma bukaci NRC ta tabbatar da tanadar da hanyoyin kiyaye yaduwar cutar coronavirus.
Kazalaika a yau ne dai ake sa ran yin gwajin sabbin jiragen ƙasan da aka kai Kaduna, amma za a fara amfani da su ne idan an ci gaba da jigilar.
A cewar sanarwar, sabbin kudin karamin kujera na jirgin N3,000, na yan kasuwa kuma N5,000, sai na masu hannu da shuni kuma N6,000.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng