Dalilin da yasa ƴan Boko Haram suke mika wuya - MNJTF

Dalilin da yasa ƴan Boko Haram suke mika wuya - MNJTF

- Wasu daga cikin tubabbun yan Boko Haram sun bayyana dalilin da yasa suka mika wuya ga sojoji

- A cewar MNJTF, yan taadan sun ce sun rashin kafuwar daular musulunci, kabilanci da rikicin shugabanci ne yasa suka tuba

- Yan taadan sun kuma ce sun gano cewa Shekau rudan su ya ke yi kuma bakar wahala kawai suke sha

Yawan rikicin shugabanci, kabilanci da rashin nasarar kafa daular musulunci da kungiyoyin Boko Haram da ISWAP su ka gaza yi ne dalilin da yasa mambobinsu ke mika wuya a cewar Sojojin Hadin Gwiwa na Kasa da Kasa, MNJTF.

A sanarwar da ta fitar a ranar Juma'a, MNJTF ta ce 'yan ta'adda guda 47 ne suka ajiye makamansu suka mika wuya ga sojojinta da ke Tafkin Chadi da kewaye.

Dalilin da yasa ƴan Boko Haram suke mika wuya - MNJTF
Dalilin da yasa ƴan Boko Haram suke mika wuya - MNJTF. Hoto daga Premium Times
Asali: Twitter

Timothy Antigha, Mai magana da yawun MNJTF da ke N’Djamena cikin wata sanarwa ya ce 'yan ta'addan tare da iyalansu sun mika wuya ga sojojin Sector 1 ta MNJTF.

Ya ce daya daga cikin 'yan ta'adan da ya amsa cewa yana daga cikin wadanda suka kai hari a Banki, Fotokol, Gambarou Ngala, New Marte, Chikun Gudu da wasu wuraren ya bayyana damuwarsa kan rashin nasara a jihadin.

DUBA WANNAN: Kano: An ƙwace kujerar ɗan majalisar APC an bawa PDP

Mr Antigha, mai mukamin kwanel, ya ambaci cewa dan ta'addan da ya mika wuya ya ce sun gaza yin nasara saboda rikicin shugabanci da kwadayin abin duniya.

"Sun fada mana cewa yaudarar mu ake kuma gwamnatin kafirai na cutar mu, amma ban ga wani banbanci tsakanin Shekau da wadanda ya ke suka ba. Kamar ma ya fi su lalacewa. Na fi jin dadi a nan domin tun lokacin da muka fito daga daji ana bamu abinci kuma ana kula da mu."

MNJTF hadin gwiwa ce ta hukumomin tsaro da aka kafa domin kawo karshen taadancin Boko Haram. Ta hada da sojoji daga Benin, Kamaru, Chadi, Nijar da Najeriya kuma hedkwatan ta na N’Djamena.

A shekarar 2015, Rundunar Sojin Najeriya ta kaddamar da atisayen ‘Operation Safe Corridor’ domin kawar da tsauraran ra'ayoyi da sauya halayen wadanda suka tuba daga ta'addancin.

'Yan kungiyar Boko Haram fiye da ISWAP fiye da 2,000 ne suka mika wuya a karkashin shirin tun kaddamar da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel