Gombe: An yanke wa tsohon shugaban karamar hukuma shekara 31 a gidan kaso

Gombe: An yanke wa tsohon shugaban karamar hukuma shekara 31 a gidan kaso

Hukumar Yaki Da Rashawa, EFCC, reshen Jihar Gombe ta yi nasara a kan Samuel Bulus Adamu a gaban Mai sharia N.I. Afolabi na Babban Kotun Tarayyaa da ke Gombe.

Kotun ta same shi da aikata dukkan laifuka bakwai da EFCC ta ke zarginsa da aikatawa kana ta yanke masa hukuncin shekara 31 a gidan gyaran hali kamar yadda LIB ta ruwaito.

Sanarwar da EFCC ta fitar yace, an fara gurfanar da tsohon shugaban karamar hukumar ta Shongomne a ranar 9 ga watan Maris na 2015 kan laifuka masu alaka da damfara, almundahar kudi da cuta.

Gombe: An yanke wa tsohon shugaban karamar hukuma shekara 31 a gidan yari
Samuel Bulus Adamu. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

Ana zarginsa da almundahanar kudi da adadinsa ya kai Naira Miliyan Casa'in da bakwai da dari shida da arba'in N97, 640, 000.00k.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace sufetan 'yan sada da wasu mutum 5 a Adamawa

Da aka karanto masa abubuwan da ake tuhumansa da aikatawa, nan take ya musanta hakan yasa EFCC ta fara shari'a da shi na tsawon shekara biyar.

Yayin shari'a, lauyoyin masu shigar da kara, A. M. Labaran and A. Y Muntaka sun kira shaidu hudu kuma sun gabatar da hujojji da ya gamsar da kotu.

Yayin yanke hukunci a ranar Alhamis 23 ga watan Yulin 2020, Mai shari'a Afolabi ya samu Adamu da laifin aikata dukkan laifuka bakwai da aka tuhume shi.

Ya yanke masa hukuncin shekara biyar ba tare a zabin biyar tara ba a laifuka na 1,2 da 4. A kan laifi na 3, an yanke masa shekara 7 da zabin tara.

An yanke masa shekaru 3 a kan laifuka na 5, 6 da 7 kowannensu ba tare da zabin biyan tara ba. Hukuncin zai fara daga ranar 10 ga watan Yulim 2020.

Mai shari'a Afolabi ya ce wanda ake yanke wa hukuncin ya biya N31, 640, 000 ga asusun karamar hukumar Shongom ta hannun kotun karkashin kulawar EFCC.

EFCC ta fara bincikar Adamu ne bayan wani kamfani TICAN Engineering Enterprises ya shigar da korafi a ofishin hukumar a ranar 9 ga watan Mayun 2011 kan zargin damfara, almundahar kudu d.s.

Hukumar yaki da rashawar ta yi bincike a kan korafin kuma daga karshe ta tabbatar da Adamu ya aikata laifin hakan ya yi sanadin hukunta shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel