Da dumi-dumi: Allah ya yi wa mahaifin gwamnan Kwara rasuwa

Da dumi-dumi: Allah ya yi wa mahaifin gwamnan Kwara rasuwa

Allah ya yi wa lauya na farko daga yankin Arewacin Najeriya, kuma mahaifin gwamnan jihar Kwara, AGF Abdul-Razaq (SAN) rasuwa.

Sanarwar da iyalansa suka fitar ta ce ya rasu ne yana da shekaru 93 a duniya a Abuja kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Allah ya yi wa lauya na farko daga Arewa, AGF Abdul-Razak rasuwa
Allah ya yi wa lauya na farko daga Arewa, AGF Abdul-Razak rasuwa
Asali: UGC

Sanarwar da ke dauke da saka hannun Dr Alimi AbdulRazak, ta ce:

"Iyalan AbdulRazak na masarautar Ilorin na jihar Kwara suna sanar da rasuwar babansu kuma ubankasa Alhaji AbdulGaniyu Folorunsho Abdul-Razaq SAN (OFR) da ya rasu yana da shekaru 93 a Abuja. An haife shi ne a 1927.

"Mutwalin Ilorin kuma Tafidan Zazzau wanda shine shugaban Kungiyar Alkalan Najeriya, ya rasu ne misalin karfe 2 na safiyar Jumaa 25 ga watan Yulin 2020 (the 4th day of Dhul-Hijjah 1441 AH.)

"Lauyan na farko daga Arewa ya rasu ya bar matarsa mai shekaru 90, Alhaja Raliat AbdulaRazak, da yaransa da suka hada da gwamnan Kwara na yanzu AbdulRahman AbdulRazaq da jikoki."

DUBA WANNAN: Ba mu da labarin sauya shekar Dogara – PDP

Har wa yau, sanarwar ta ce iyalansa za su sanar da lokacin da za ayi janaizarsa nan da kankanin lokaci.

Allah ya jikansa da rahama ya gafarta masa. Amin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel