Kano: An ƙwace kujerar ɗan majalisar APC an bawa PDP

Kano: An ƙwace kujerar ɗan majalisar APC an bawa PDP

Kotun zaben raba gardama na majalisar jihar Kano a ranar Juma'a ta soke zaben Magaji Zarewa na jam'iyyar APC mai wakiltar mazabar Rogo a jihar kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Jibril Falgore, dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya yi kara a kotu inda ya ke kallubalantar nasarar Zarewa a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 25 ga watan Janairu.

Sauran wadanda ya yi karar a kotun sun hada da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, da jam'iyyar APC kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ta ruwaito.

Kotu ta soke zaben ɗan majalisar APC a Kano
Kotu ta soke zaben ɗan majalisar APC a Kano. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Musulmi sun yi sallar Juma'a ta farko a masallacin Hagia Sofia tun shekaru 86 da su ka gabata (Hotuna)

Alkalan uku karkashin jagorancin, Mai sharia A.M. Yakubu dukkansu sun amince da soke zaben Mr Zarewa a kan dalilin cewa bai yi murabus ba daga hukumar kula da shigo da magunguna da sauran ababen sha na jihar Kano kwanaki 30 kafin zabe ba, kamar yadda yake a dokar tsayawa takara ta INEC.

Kotun ta yanke hukuncin cewa Mr Falgore na jam'iyyar PDP shine hallastaccen zababben dan majalisa mai wakiltan mazabar Rogo.

Kotun ta umurci magatakardan majalisar jihar Kano ya rantsar da Jibril Falgore a matsayin zababben mamba mai wakiltar mazabar Rogo nan take ba tare da bata lokaci ba.

Lauyan wanda ya shigar da kara, Ibrahim Waru, a baya ya shaidawa kotu cewa Mr Zarewa ba bai cancanta ba ya sake takara a zaben rada gardama da za ayi a mazabar da Rogo.

Mr Waru ya roki kotun ta soke zaben Mr Zarwa inda ya bayyana cewa wanda aka yi karar bai yi murabus daga matsayinsa ba a matsayin shugaban Hukumar kula da shigo da magunguna da ababen sha kwanaki 30 kafin zabe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel