Ba mu da labarin sauya shekar Dogara – PDP

Ba mu da labarin sauya shekar Dogara – PDP

Jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) a jihar Bauchi ta ce tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Yakubu Dogara bai riga ya sanar da ita cewa ya fice daga jam'iyyar ba.

Shugaban jam'iyyar, Alhaji Hamza Akuyam, yayin da ya ke martani a kan sauya rahotan sauya shekar da Dogara ya shaidawa The Nation a wayar tarho cewa PDP na jiran tsohon kakakin ya aiko mata da wasika.

"Ba mu samu wasika daga wurinsa na cewa ya fita daga jam'iyyar mu ba kuma don an gan shi da shugaban kasa ba wani abin mamaki bane domin ai shi tsohon kakakin majalisar tarayya ne.

"Watakila akwai abinda ya ke son ya tattauna da shi ne amma idan har ya sanar da mu a hukumance cewa ya bar jam'iyyar mu, za mu yi tsokaci a kan batun. A halin yanzu muna jirar wasika daga wurin shi."

Ba mu da labarin sauya shekar Dogara – PDP
Hon. Yakubu Dogara
Asali: UGC

Shugaban kwamitin riko na jamiyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni da ya yi wa Dogara rakiya ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa a ranar Juma'a ne ya tabbatar da cewa dan majalisar Bauchin ya koma APC.

Dab da babban zaben shekarar 2019 ne Dogara ya fice daga jam'iyyar APC ya koma jam'iyyar adawa ta PDP.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Jam'iyyar PDP ta nemi Buhari ya yi murabus, ta bayar da dalili

Dukkan kokarin da aka yi na sanin dalilin da yasa Dogara ya sauya sheka ya ci tura domin mashawarcinsa na musamman kan watsa labarai, Turaki Hassan bai amsa kirar waya da sakon da aka aike masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

A shekarar 2018 Dogara ya fice daga jamiyyar APC ya koma PDP sakamakon rashin jituwa da suka samu da tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar.

A baya bayan nan tsohon kakakin majalisar ya jagorancin kwamitin tantance wadanda za su fafata a zaben fidda gwani na neman tikitin takarar gwamna a PDP a jihar Ondo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel