'Yan bindiga sun sace sufetan 'yan sada da wasu mutum 5 a Adamawa

'Yan bindiga sun sace sufetan 'yan sada da wasu mutum 5 a Adamawa

Wasu 'yan bindiga sun sace dan sanda mai mukamin sufeta, matan wasu fitaccen mafarauci da wasu mutane biyu a garin Koma da ke jihar Adamawa kamar yadda The Nation ta ruwaito.

'Yan bindigan sun sace mutane shidan ne daga gidajensu da tsakar dare a garin na Koma da ke karamar hukumar Jada ta jihar Adamawa.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa maharan a safiyar ranar Alhamis sun kashe mutum daya da ake tunanin ya zame barazana gare su.

Rahotanni sun ce yan bindigan masu yawa sun shiga garin na Koma sannan suka fara bi gidajen wadanda suke son sacewa daya bayan daya suna daukan su.

'Yan bindiga sun sace sufetan 'yan sada da wasu mutum 5 a Adamawa
'Yan bindiga sun sace sufetan 'yan sada da wasu mutum 5 a Adamawa. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Jam'iyyar PDP ta nemi Buhari ya yi murabus, ta bayar da dalili

"Azzaluman nan sun shigo sun tafi cikin kwanciyar hankali ba tare da wani ta taka musu birki ba," a cewar wata majiya.

Wadanda aka sace din sune Sufeta Yakubu, Hon Bulus Geoffrey (Kansilar mazabar Koma); Hammanjida Hammanjalo; Hajiya Amina, da kuma matan fitaccen mafarauci Mallam Hassan su biyu.

Bisa ga alamu dai yan bindigan sun fi kai wa yan sanda da mafarauta hari ne.

A ranar 7 ga watan Yuli, an sace wani sufetan yan sanda a babban titin Numan zuwa Yola.

Akwai yiwuwar suna kai wa mafarautan hari ne domin mafarautan suna hada kai da yan sanda wurin yakar yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar Adamawa.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce jamian rundunar sun bi sahun maharan da nufin ceto wadanda aka sace.

"Yan sanda tare da mafarautan garin suna nan yanzu suna bin sahun wadanda ake zargin sun aikata laifin.

"Muna tabbatar wa dukkan wanda abin ya shafa cewa za mu ceto wadanda aka sace kuma mu kama wadanda ake zargin," a cewar kakakin yan sandan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel