Mutane sun maƙale bayan bene ya rufta a Legas (Hotuna)

Mutane sun maƙale bayan bene ya rufta a Legas (Hotuna)

Wasu mutane sun maƙale bayan wani bene mai hawa biyu da ke unguwar Ebute Metta a Legas ya rufta da su.

Ginin ya da rufta a ranar Juma'a yana kallon Cibiyar Lafiya ne da ke kan layin Maƙabarta kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Jami'an Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Legas, LASEMA, sun isa wurin suna ƙoƙarin ceto mutanen da suka maƙale cikin ginin.

Mutane sun maƙale bayan bene ya rufta a Legas
Mutane sun maƙale bayan bene ya rufta a Legas. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

Mutane sun maƙale bayan bene ya rufta a Legas
Mutane sun maƙale bayan bene ya rufta a Legas
Asali: Twitter

An ceto mutum biyu daga ginin da ya rufta a gida mai lamba 95 Layin Makabarta da ke Ebutte Metta a Legas.

Nosa Okunbor, Kakakin Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar Legas, ya ce masu bayar da taimakon farko sun yi wa wadanda aka ceto daga ginin magani a nan take.

DUBA WANNAN: Musulmi sun yi sallar Juma'a ta farko a masallacin Hagia Sofia tun shekaru 86 da su ka gabata (Hotuna)

Gidan mai bene uku da ya rufta a ranar Juma'a an gina shi ne tun shekaru 25 da suka gabata.

"Da isar mu wurin da abin ya faru, mun gano cewa ginin mai bene uku ya rufta," in ji shi, inda ya kara da cewa a halin yanzu ba za a iya cewa ga dalilin da yasa ginin ya rufta ba.

"An ceto wata dattijuwa da yarinya da ginin ya rufta musu duk da cewa sun samu kananan rauni amma masu kawo taimakon farko sun yi musu magani kafin aka sallame su.

"Gidan da ya rufta da aka yi shekaru 25 a 95 Layin Makabarta da ke tsakanin Layin Legas da Abeokuta a Ebute Metta a cewar wasu mazauna unguwar ya fara nuna alamar gajiyawa," a cewar LASEMA.

Hukumar ta ce akwai dakuna shida da falo kananan da wani mai kula da gine gine ya sake ginawa.

Ibrahim Farinloye, Mukadashin shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa, NEMA, ya ce mutane da yawa ba su mutu ba saboda mafi yawancin masu gidan sun fita a lokacin da abin ya faru.

Mr Okunbor ya ce LASEMA tana cigaba da bincike a kan lamarin.

Ya ce hukumomin da abin ya shafa suna can suna bayar da gudunmawar da ta dace.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel