Yanzu-yanzu: Jam'iyyar PDP ta nemi Buhari ya yi murabus, ta bayar da dalili
Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus saboda zargin rashawa da ake a hukumomin tarayya.
Shugaban Jam'iyyar adawar, Prince Uche Secondus ne ya yi wannan kirar a wani hirar da ake yi da shi a kafar watsa labarai a Abuja kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Ya ambaci binciken rashawar da ake yi a hukumomin NDDC, MIC, NEDC, NSITF, EFCC da wasu inda ya ce da ƙyar Najeriya ke numfashi a karkashin mulkin Buhari.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Alkali ya raba aure saboda mata ta ce mijin “ɗan ƙarya ne”
Secondus ya ce rashawa ya zama ruwan dare a kasar yayin da Buhari ke cigaba da kawar da kansa.
Ya yi iƙirarin cewa Buhari ya yi watsi da alƙawarin da ya yi na yaƙi da rashawa yayin yaƙin neman zabensa na 2015 da 2019.
Ku saurari karin bayani ...
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng