Musulmi sun yi sallar Juma'a ta farko a masallacin Hagia Sofia tun shekaru 86 da su ka gabata (Hotuna)

Musulmi sun yi sallar Juma'a ta farko a masallacin Hagia Sofia tun shekaru 86 da su ka gabata (Hotuna)

Makonni biyu da suka wuce, wata kotu a ƙasar Turkiyya ta soke wata doka da ta mayar da wani tsohon masallaci zuwa gidan ajiye kayan tarihi.

Soke dokar ya bawa musulmi dama su karɓi ginin a kuma fara salla ciki kamar yadda aka saba a baya kamar yadda TRT ta ruwaito.

Bayan shekaru 86 a matsayin gidan tarihi, musulmi za su cigaba da salla a Hagia Sophia da ke birnin Istanbul.

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan da wasu ƴan siyasa daga jam'iyyun Justice da Development da ma wasu ƴan siyasar za su halarci bikin buɗe masallacin.

Musulmi sun yi sallar Juma'a ta farko a masallacin Hagia Sofia tun shekaru 86 da su ka gabata
Shugaban Turkiyya, Tayyip Erdogan a gaban masallacin Hagia. Hoto daga TRT
Asali: Twitter

Musulmi sun yi sallar Juma'a ta farko a masallacin Hagia Sofia tun shekaru 86 da su ka gabata
Musulmi sun yi sallar Juma'a ta farko a masallacin Hagia Sofia tun shekaru 86 da su ka gabata. Hoto daga TRT
Asali: Twitter

Shugabanni da manyan baƙi daga ƙasashe kamar Azerbaijan da Qatar suma za su halarci bikin buɗe masallacin.

Za a bude taron da addu'o'i da kaburbura da sallatin Manzon Allah don gode wa Allah bisa wannan nasara da ya bawa al'ummar musulmin ƙasar.

DUBA WANNAN: Alkali ya raba aure saboda mata ta ce mijin “ɗan ƙarya ne”

Tun safiyar yau Juma'a, masallata sun fara tururuwa zuwa masallacin dauke da dadduma a hannunsu yayin da ƙira'ar Ƙur'ani mai girma ke tashi daga cikin masallacin.

An taƙaita adadin mutanen da za su shiga cikin masallacin domin tabbatar da dokar bayar da tazara don daƙile yaɗuwar korona.

Musulmi sun yi sallar Juma'a ta farko a masallacin Hagia Sofia tun shekaru 86 da su ka gabata
Hagia Sofia. Hoto daga TRT
Asali: Twitter

Mutane da dama sun samu wurare kusa da masallacin domin hallartar sallar Juma'ar wasu ma har a rufin saman gidaje suka shimfida sallayarsu.

Da farko, jami'an tsaro sun rufe hanyoyin zuwa masallacin domin taƙaita adadin mutanen da za su halarci masallacin don yin sallar Juma'a.

A ranar Alhamis ne Shugaba Erdogan ya buɗe masallacin a hukumance mai ɗauke da suna "Hagia Sophia Grand Mosque".

Wani mutum mazaunin birnin Sirrt da TRT ta zanta da shi ya bayyana irin farin cikin da ya ke ciki sakamakon bude masallacin.

"Ina matukar farin cikin ganin wannan rana da zan yi sallar a nan bayan shekaru 42," a cewar Bedrettin Kayar mai sayar da kayan ƙawata ɗaki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164