Hajj 2021: NAHCON za ta fara karbar kudin maniyyata a watan Satumba

Hajj 2021: NAHCON za ta fara karbar kudin maniyyata a watan Satumba

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta sanar da cewa, a ranar 9 ga watan Satumba za ta fara yi wa maniyyatan aikin hajjin badi rajista.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, shugaban hukumar NAHCON na kasa, Zikrullahi Hassan, shi ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Abuja a ranar Alhamis.

Alhaji Hassan ya ce hukumar za ta bude wani sabon shafi na yanar gizo domin saukaka wa maniyyatan rajista.

Ya shawarcin maniyyatan aikin hajjin na badi da su fara tanadar kudadensu tun yanzu domin yin 'adashin gata' a asusun hukumar.

Hajj 2021: NAHCON za ta fara karbar kudin maniyyata a watan Satumba
Hajj 2021: NAHCON za ta fara karbar kudin maniyyata a watan Satumba
Asali: UGC

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa, hukumomin Saudiyya sun soke aikin hajjin bana ga maniyyata daga kasashen ketare sakamakaon fargabar annobar korona.

Sai dai gwamnatin kasar ta ce za a bari duk wani musulmi da ke zaune a kasar wadanda suka nuna bukata su yi aikin hajjin ko da kuwa ba 'yan asalin kasar bane.

Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Kano, KSPWB, ta ce a shirye ta ke ta mayar wa dukkan maniyyatan da suka biya kudin kujerar hajjin bana kudadensu.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa ta tafi hutun shekara, za ta dawo ranar 15 ga Satumba

Babban sakataren hukumar, Muhammad Abba, ne ya bayar da wannan tabbacin hakan a wata hira da ya yi tare da manema labarai a birnin Kanon Dabo.

Alhaji Abba ya shaidawa manema labarai cewa maniyyatan da ke son a mayar musu da kudadensu za a mayar musu kana wadanda ke son ajiye kudin don hajjin badi suna iya barin kudinsu a hannun hukumar.

Ya bayar da tabbacin cewa, babu wani maniyyaci cikin wadanda suka biya kudin aikin hajjin na bana da za su rasa ko da sisin kwabo na kudadensu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel