Kotu ta bai wa ma'aurata damar sanya wa dan su suna 'Shaidan'

Kotu ta bai wa ma'aurata damar sanya wa dan su suna 'Shaidan'

Wasu ma'aurata a kasar New Zealand daga yankin Chesterfield, Derbyshire sun yi nasarar wata gwagwarmaya a kotu inda aka amince da su saka wa dan su mai watanni hudu da haihuwa suna "Iblis" bayan an so hana su sanya wa dan wannan sunan.

Dan, wanda yake aiki a wani kamfani ya kai kokensa a kan cewa an wulakanta su shi da matarsa bayan suka je yi wa dan nasa da suka haifa yayin kulle rijista.

Ya ce, "muna jin dadin za mu je yi mishi rijista amma da muka isa sai matar ta kalle mu a wulakance.

"Ta ce ba zai taba samun aiki ba kuma malamai ba zasu koyar da shi ba. Na yi kokarin yi mata bayanin cewa bamu da addini kuma sunan a Girka yana nufin "mai kawo haske ko kuma safiya" amma ta ki saurarar mu.

"Ta ce shari'ar New Zealand bata aminta a sakawa da wannan sunan ba. Saidai mu je mu sauya mishi suna ko a gida mu dinga kiran shi da Iblis."

Bayan kafewa da ma'auratan suka yi a kan sai sun saka wa dan su Iblis, an bukacesu da su fice daga wurin rijistar.

Kotu ta bai wa ma'aurata damar sanya wa dan su suna 'Shaidan'
Kotu ta bai wa ma'aurata damar sanya wa dan su suna 'Iblis'. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kurunkus: Akpabio ya yi fallasa, ya bayyana 'yan majalisar da suka karbe kwangilar NDDC

Dan ya kara da cewa, "mun sha mamaki da abinda tayi mana. Amma daga karshe ta yi rijistar cike da fushi. A gaskiya muna tunanin suna ne mai kyau kuma babu masu irin shi. Ba mu yi tsammanin hakan za ta faru ba."

Kasar New Zealand wacce ke da tsauraran matakai a kan saka wa yara suna, ta saka Iblis a cikin sunayen da bata amince a sakawa yara ba tun a 2013.

Kakakin Derbyshire ya ce mai rijistar ta yi abinda ya dace da ta sanar da ma'auratan cewa ba a amince da wannan sunan ba.

"Ta yi daidai da ta ki yin rijistar saboda ta san cewa wannan sunan bashi da amfani kuma zai iya zama matsala gareta idan tayi rijistar. Sannan yaron zai zama tamkar mujiya a cikin mutane."

Bayan da mai rijistar ta tuntubi babban ofishin su, an tabbatar mata da cewa tayi daidai kuma hakan gata ne ga jaririn.

"Duk da shawarar, ma'auratan sun ce suna son sunan kuma haka aka yi musu rijistar," kakakin yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel