Majalisar Dattawa ta tafi hutun shekara, za ta dawo ranar 15 ga Satumba

Majalisar Dattawa ta tafi hutun shekara, za ta dawo ranar 15 ga Satumba

A ranar Alhamis ne majalisar dattawan Najeriya ta dage zamanta har zuwa ranar 15 ga watan Satumba domin bai wa mambobinta damar samun hutunsu na shekara-shekara da aka saba a al'ada.

Shugaban majalisar dattawan Sanata Ahmad Lawan, shine ya sanar da hakan bayan wani zaman shugabannin majalisar da aka gudanar a birnin Abuja.

Sai dai Sanata Lawan ya ce ba tare da hanzari ba, kwamitoci daban-daban da za su ci gaba tattaunawa kan wasu muhimman ayyuka da ke bukatar kulawa ta gaggawa, za su ci gaba gudanar da zama yayin da bukata ta taso.

Ya umarci kwamitin majalisar da aka ratayawa hakkokin kula da kudi, da ya hada hannu-da-hannu da Ministar Kudi, Kasafi da tsare-tsaren ci gaban kasa, Zainab Ahmed, to min shirya kudirin kasafin kudin kasar na badi.

Shugaban Majalisar Dattawa; Sanata Ahmed Lawan
Hoto daga jaridar guardian
Shugaban Majalisar Dattawa; Sanata Ahmed Lawan Hoto daga jaridar guardian
Asali: Twitter

A wani rahoto da jaridar Legit.ng ta ruwaito, sakataren APC na rikon-kwarya, Sanata John Udoedeghe ya yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyarsa da su yi kokari wajen ganin sun samu nasara a zabe mai zuwa.

John Udoedeghe ya ce zuwa babban zaben 2023, lokacin da mutane za su shige inuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya wuce.

Jaridar Punch ta rahoto jagoran jam’iyyar mai mulki ya na wannan kira a lokacin da ya zauna da wata kungiya ta magoya bayan APC a karkashin Frank Ossai.

An yi wannan zama ne a babban sakatariyar jam’iyyar APC da ke birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 22 ga watan Yuli, 2020.

Udoedeghe ya ke cewa: “Dukkanku da ke siyasar kasa; ku tabbatar an cigaba da damawa da ku a mazabunku, da kananan hukumomi, da kuma jihohinku.”

KARANTA KUMA: An samu nasarar yi wa Sarki Salman tiyata a mafitsara

A 2023 ne shugaba Buhari zai kammala wa’adinsa na shekaru takwas. Ana tunanin cewa APC ta na samun damar lashe zababbuka a matakai da-dama saboda sunansa.

Sanatan na jihar Edo ya gargadi magoya bayan jam’iyyar da cewa: “A zaben 2023, shugaba Muhammadu Buhari ba zai fito a cikin masu takara ba.”

‘Dan siyasar ya kuma shaidawa fusatattun ‘yan jam’iyyar APC cewa kwamitinsu na rikon kwarya a shirya ya ke da ya yi wa kowa adalci wajen dinke barakar da jam’iyyar ke fama da ita.

Kafin nan, shugaban tafiyar, Frank Ossai ya yi kira ga kwamitin rikon da ya duba aikin da Sanata Ken Nnamani ya taba yi domin kawo zaman lafiya a APC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel