Alkali ya raba aure saboda mata ta ce mijin “ɗan ƙarya ne”

Alkali ya raba aure saboda mata ta ce mijin “ɗan ƙarya ne”

Wata kotun gargajiya da ke zamanta a Mapo Ibadan a ranar Alhamis ra raba auren wasu ma'aurata da suka yi shekaru 14 tare a kan dalilin sakaci da rayuwar karya da mijin ke yi.

Shugaban kotun, Cif Ademola Odunade ya raba auren Bukola Akinyode da Azeez saboda a samu zaman lafiya da lumana kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Odunade ya bawa wanda aka yi karar ikon rike yara biyu sannan ya bawa wadda ta yi karar sauran yaran biyu.

Ya umurci Azeez ya rika biyan tsohuwar matarsa N10, 000 duk wata a matsayin kudin ciyarwa kana shi zai rika biyan kudin makarantarsu da kuma kula da walwalarsu.

Kotu ta raba aure saboda mijin “ɗan ƙarya ne”
Kotu. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Tunda farko, Bukola, mai sanaar treda da ke zaune a Omi-Apata a Ibadan ta ce bata son cigaba da zaman aure da mijinta Azeez saboda irin wahahalun da ta ke sha a hannunsa.

Ta kara da cewa mijinta ya kan yi mata rauni da adda a duk lokacin da suka samu rashin jituwa.

DUBA WANNAN: Babu gudu babu ja da baya kan yi wa Fani–Kayode sarauta – Masarautar Shinkafi

"Wasu lokutan, Azeez ya kan rufe ni a waje sai na dangana da kwana a wani masallaci da ke kusa da mu saboda tsaro.

"Azeez yana rayuwa irin ta bushasha a unguwarmu. Yana shan barasa na fitar hankali kuma baya kulawa da yaransa.

"Irin rayuwar da ya ke yi kan saka mutane su rika tunanin muna cikin daula amma ba su san cewa matarsa da yaransa suna fama da yunwa ba.

"Kuma duk lokacin da iyaye na suka bani jari domin in fara sanaa, Azeez ya kan amshe kudin daga hannu na," a cewar Bukola.

Wanda aka yi kararsa ya amince da bukatar raba auren amma ya musanta zargin da tayi masa.

Azeez, direban babban mota ya amince a raba auren domin matarsa tana da wuyar sha'ani.

"Da gaske ne wasu lokutan na kan ranci kudi a hannunta amma na kan biya bashin duk lokacin da na karba amma duk da haka sai ta rika damu na kamar tana bi na bashi.

"Dalilin da yasa na rufe ta a waje shine saboda bata min biyayya.

"Bayan da yan fashi suka kawo mana hari wani rana, na yanke shawarar kowa ya rika dawowa gida da wuri amma Bukola ta kan yi dare tana hada hada da kwastomominta galibinsu maza.

"Ina kulawa da bukatun yara na," a cewar Azeez.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel