Niger: Almajirai 64 sun warke daga cutar korona

Niger: Almajirai 64 sun warke daga cutar korona

Gwamnatin Jihar Niger a ranar Laraba ta sanar da cewa almajiri 64 da suka kamu da korona a jihar sun warke, an kuma mayar da su gidajensu don sada su da iyalansu.

Kwamishinan Lafiya da Ayyukan Asibiti, Dr. Mohammed Makusidi ya sanar da hakan yayin da ya ke amsa tambayoyin ƴan jarida a Minna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce, "Kamar yadda muka fadi a baya, muna da mutum 166 da suka kamu da Covid-19 cikinsu har da almajirai.

Almajirai 64 sun warke daga cutar korona a Niger
Almajirai 64 sun warke daga cutar korona a Niger. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Sultan ya yi kira ga musulmi suyi sallar Idi a masallatan Juma'a

"An yi wa almajirai 1075 gwajin coronavirus cikinsu 64 suna dauke da kwayar cutar.

"Sai dai abin farin ciki yanzu dukkansu 64 sun warke kuma an sada su da iyalansu."

Ya ce waɗanda ba ƴan asalin jihar bane suma an mayar da su johohinsu na asali don sada su da iyalansu.

Makusidi ya ce kawo yanzu an gwada mutum 1,778 gwajin Covid-19 cikinsu 166 sun kamu, amma, "A yanzu, ba mu da ko majinyanci ɗaya a cibiyar killace masu jinya saboda duk mun sallame su yayin da tsirarun da suka rage an mayar da su asibitoci."

A baya, Gwamna Abubakar Sani Bello, yayin jawabin manema labarai ya ce ɗalibai da ma'aikata su cigaba da zama a gida har zuwa wani lokaci nan gaba.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne bayan shugaban kwamitin yaƙi da Covid-19 na jihar Ibrahim Matane ya kammala nasa jawabin.

A wani labarin daban, kun ji cewa Sarkin Musulimi Sa'ad Abubakar ya bukaci hakimai da shugabannin addini suyi limancin sallar Idi a masallatan Juma'a a maimakon zuwa filayen sallar Idi.

Sultan din ya bayar da wannan shawarar ce yayin da ya ke sanar da cewa a ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2020 ce ranar babbar Sallah kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

A cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba 22 ga watan Yuli, Sultan Abubakar ya yi kira ga alummar musulmi suyi adduo'in zaman lafiya da samun cigaba a kasar.

Sarkin musulmin ya kuma ce za ayi sallar Idin na bana ne a ranar Jumaa 31 ga watan Yuli da ya yi daidai da 10 ga watan Zulhijja ta 1441 AH.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel