Ban ce an bawa ƴan majalisar 60% na kwangilar NDDC ba - Akpabio

Ban ce an bawa ƴan majalisar 60% na kwangilar NDDC ba - Akpabio

- Ministan Neja Delta, Godswill Akpabio ya rubuta wa Majalisar Wakilai ta Tarayya wasika a ranar Alhamis

- A cikin wasikar da Kakakin Majalisa, Femi Gbajabiamila ya karanto, Akpabio ya ce ba a fahimce shi bane kan batun kwangilar NDDC

- Ministan ya ce bai ce kaso 60 na kwangilar hukumar NDDC 'yan majalisar wakilai na tarayyar aka bawa ba

Ministan Harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio ya musanta cewa ya ce mafi yawancin kwangilolin da aka yi a Hukumar Cigaban Yankin Niger Delta, NDDC, ƴan majalisa aka bawa.

An zargi Akpabio ta zargin cewa kashi 60 cikin 100 na kwangilolin hukumar ta NDDC ƴan majalisar tarayya aka bawa kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Sai dai a wasikar da ya aike wa majalisar wakilai a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuli, ministan ya ce ya ambaci wannan kason ne a lokacin da ya ke amsa tambayar wani mamban kwamitin binciken.

Ban ce an bawa yan majalisar 60% na kwangilar NDDC ba - Akpabio
Ban ce an bawa yan majalisar 60% na kwangilar NDDC ba - Akpabio. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An bawa Sarkin Shinkafi wa'addin awa 24 ya kwace sarautar da ya bawa Fani-Kayode

Kakakin Majalisar Femi Gbajabiamila ne ya karonto wasikar da ministan ya aike wa majalisar a yayin zamanta na ranar Alhamis.

Bayan karanto wasikar, Kakakin Majalisar bai yi karin bayani a kan barazanar da suka yi na karar ministan a kotu ba.

Akpabio ya ce hukumar ta NDDC ta ta yi wani kwangila ba a shekarar 2020 tunda ba a amince da kasafin kudin hukumar ba yayin da kasafin 2019 da aka amince da shi a watan Afrilu ba riga an aiwatar da shi ba.

A baya, mun kawo muku cewa ta Majalisar ta yi barazanar yin karar Ministan Niger Delta Godswill Akpabio a kotu kan ikirarin da ya yi na cewa ƴan Majalisar sun karbi kwangiloli masu yawa a NDDC.

Ministan ya yi wannan ikirarin ne yayin da ya gurfana a gaban kwamitin majalisar da aka kafa domin binciken kudaden da ake kashewa a hukumar da ake ganin ya wuce hankali.

Daily Trust ta ruwaito cewa Majalisar, a zaman ta na ranar Talata, ta kallubalanci ministan ya wallafa sunayen ƴan majalisar da ya yi ikirarin sun karbi kwangilar a NDDC.

Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila, a ranar Alhamis ya ce Majalisar za ta garzaya kotu tayi karar Akpabio idan ya gaza kawo hujja a kan ikirarin da ya yi a baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164