Hadimin Ayade ya yanke jiki ya fadi ya mutu

Hadimin Ayade ya yanke jiki ya fadi ya mutu

Mashawarci na musamman ga Gwamnan Cross Rivers Ben Ayade a kan Albarkatun Rayuwa, Edet Okon Asim ya riga mu gidan gaskiya.

Rahotanni sun ce ya yanke jiki ya fadi ne a cikin motarsa da ke Eta Agbor a garin Calabar a yammacin ranar Talata.

Wata majiya daga iyalan mammacin ta ce yana fama da ciwon matsalar numfashi wato Asthma duk da cewa a halin yanzu ba a tabbatar da ainihin abinda ya yi sanadin mutuwarsa ba.

Hadimin Ayade ya yanke jiki ya fadi ya mutu
Hadimin Ayade ya yanke jiki ya fadi ya mutu
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An bawa Sarkin Shinkafi wa'addin awa 24 ya kwace sarautar da ya bawa Fani-Kayode

Okon Asim ya taba rike mukamin kwamishinan labarai a jihar ta Cross River.

Tuni dai an dauki gawarsa an kai ta zuwa dajin ajiye gawarwarki a asibiti.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, 'Yan bindiga sun kashe dagajin kauyen Gora Gan da ke karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna da wasu mutane tara.

Wannan na zuwa na kimanin awa 24 bayan kashe wasu matasa 21 yayin bikin daurin aure a kauyen Kukum Daji da ke karamar hukumar Kaura.

The Nation ta ruwaito cewa har da wani yaro mai shekara shida cikin wadanda aka kashe a harin na baya bayan nan tare da jikkata wasu mutane da dama.

Wani wanda abin ya faru a idonsa ya ce yan bindiga kimanin su 20 ne suka kai farmaki kauyen misalin karfe 7 na yamma a ranar Litinin suka fara harbe harbe.

Mataimakin shugaban kungiyar Kirista ta Najeriya, CAN, reshen karamar hukumar Zangon LKataf, Fasto Isaac Ango-Makama ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce an kone gidaje da dama yayin harin.

Ya ce an kai gawarwakin wadanda suka mutun zuwa babban asibitin garin Zonkwa yayin wadanda suka jikkata kuma an kai su wani asibitin inda ake musu magani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel