'Yan bindiga sun sake bindige wani ɗan kasuwa har lahira a Jigawa

'Yan bindiga sun sake bindige wani ɗan kasuwa har lahira a Jigawa

Wasu 'yan bindiga a ranar Litinin sun kashe wani dan kasuwa, Magaji Mukhtar da dan banga, Ibrahim Sule, yayin wata hari da suka kai a karamar hukumar Garki ta jihar Jigawa kamar yadda 'yan sanda suka fadi.

Kakakin 'yan sandan Jigawa, Audu Jinjiri ya shaidawa Premium Times cewa maharan sun bindige dan kasuwar har lahira a cikin gidansa da ke garin Garki saboda ya hana su kudi.

Amma mazauna garin sun ce 'yan bindigan sun harbi Mukhtar ne a gaban matansa biyu bayan ya ki yarda su tafi da shi duk da cewa ya basu wasu kudade da ba a tabbatar da adadinsu ba.

'Yan bindiga sun sake bindige wani ɗan kasuwa har lahira a Jigawa
'Yan bindiga sun sake bindige wani ɗan kasuwa har lahira a Jigawa. Hoto daga Channels TV
Asali: UGC

"Ba su gamsu da kudin da ya basu ba don haka suka nemi tafiya da shi, bai amince ba sai suka bindige shi har lahira," a cewar wani majiya daga iyalan mamacin da ba za a iya bayyana sunansa ba saboda tsaro.

DUBA WANNAN: An bawa Sarkin Shinkafi wa'addin awa 24 ya kwace sarautar da ya bawa Fani-Kayode

Wani dan banga da ke zaune a unguwar, Ibrahim Sule shima ya rasa ransa a yayin da ya yi kokarin tunkarar maharan bayan da ya ji karar harbin bindiga kuma ya tafi domin ya duba abinda ke faruwa.

'Yan sanda sun ce sun isa wurin da abin ya faru sun kuma bi sahun maharan a tsakar daren inda suka yi musayar wuta amma maharan sun tsere a kan babura.

Majiyar Legit.ng har ila yau ta ruwaito yadda masu garkuwa suka sace wani dan kasuwa, Yusuf Maitama a karamar hukumar Ringim yana kwance yana jinya.

Rahotanni sun bayyana cewa ya mutu a hannun masu garkuwar duk da an biya kudin fansa Naira miliyan biyar.

Kafin rasuwarsa, Maifata shima sanannen dan kasuwa ne kuma dan kwangila da ke samar wa makarantun sakandare na jihar Jigawa abincin da ake dafa wa dalibai.

Wannan kashe kashen ya tayar da hankulan mutane da ke zargin akwai wasu 'yan leken asiri da ke sanar da maharan game da 'yan kasuwan da ke jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel