Kungiyoyin Ƴan Jaridar Najeriya sun karrama Isa Funtua (Hoto)

Kungiyoyin Ƴan Jaridar Najeriya sun karrama Isa Funtua (Hoto)

Kungiyar 'Yan Jarida ta Najeriya ta saka wa sabon ginin Cibiyar Nazarin Aikin Jarida da ta gina sunan marigayi Mallam Ismaila Isa Funtua.

Mallam Isa Funtua, wanda shine uban kungiyar Cibiyar Koyan Aikin Jarida da Kungiyar Masu Gidajen Jaridu ta Najeriya, (NPAN) ya rasu ne a ranar Litinin da dadare yana da shekaru 78.

A sanarwar da ta fitar a ranar Laraba, Kungiyar Masu Aikin Jarida ta Najeriya da ta hada da Kungiyar Masu Gidajen Jarida (NPAN), Kungiyar Masu Tace Labarai ta Najeriya, (NGE), da Kungiyar Yan Jarida ta Kasa, (NUJ), ta ce an saka wa sabon ginin hukumar da ke Legas suna Ismaila Isa House.

An karrama makkusancin Buhari, Ismaila Isa Funtua
An karrama makkusancin Buhari, Ismaila Isa Funtua. Hoto daga This Day
Asali: Twitter

Sanarwar ta ce anyi hakan ne domin karrama rayuwa da ayyukan da marigayi goggagen dan jaridan ya yi.

DUBA WANNAN: Budurwa ta bindige saurayinta saboda ya ki biye mata suyi cacar baki

Sanarwar ta ce: "Saboda gudunmawar da ya bayar wurin cigaba da kwato yancin 'yan jarida a Najeriya da duniya, Kungiyar 'Yan Jaridun Najeriya na farin cikin saka wa sabon ginin Cibiyar Nazarin Aikin Jarida da ke Adeyemo Alakija Street, Victoria Island, Lagos suna Ismaila Isa House don karrama Mallam Ismaila Isa Funtuna, OFR, Mni, da ya rasu a ranar Litinin July 20, 2020 bayan yi wa Najeriya hidima a bangaren siyasa, kasuwanci da aikin jarida.

"Gudunmawar da ya bayar wurin cigaban aikin jarida a Najeriya ba zai misaltu ba: Sun hada da kafa Democrat Newspapers; Shugabancin NPAN a lokacin kasa na cikin rikici da zama uban kungiyar.

"Saura sun hada da gudunmawa da ya bawa Cibiyar Yan Jarida ta Kasa da Kasa a matsayin mamba na kwamitin amintattu; gudunmawa wurin koyar da aikin jarida a matsayinsa na shugaban kwamitin shugabannin Cibiyar Aikin Jarida ta Najeriya da sauransu.

"Za mu yi kewar Samaila Isa Funtua, 1942 -2020, amma ba za mu taba mantawa da shi ba."

A wani rahoton da Legit,ng ta wallafa, Uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta magantu a kan rawar da marigayi Mallam Isma'il Isa Funtua ya rika taka wa a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Hajiya Aisha a ranar Laraba, ta fayyace yadda Marigayi Mallam Funtua ya jajirce wajen goyon bayan mata masu damawa a harkokin siyasa musamman a tsawon shekaru hudun da suka gabata.

Uwargidan shugaban kasar ta ce Marigayi Funtua ya rika faɗi-tashin ganin an bai wa mata akalar jagoranci a Hukumomi da Cibiyoyi a gwamnatin Buhari.

Matar shugaban kasar ta bayyana hakan ne cikin wani sakon na alhini kan mutuwar Mallam Funtua da ta wallafa a shafukanta na dandalan sada zumuta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel