Da duminsa: Boko Haram ta saki bidiyon kisan gilla da suka yi wa ma'aikatan SEMA da mai gadi

Da duminsa: Boko Haram ta saki bidiyon kisan gilla da suka yi wa ma'aikatan SEMA da mai gadi

'Yan ta'addan Boko Haram a ranar Laraba sun yi wa ma'aikatan taimako hudu da mai gadi daya da suka sace a wata daya da ya gabata, kisan gilla.

Bayan sace ma'aikatan da mayakan ta'addancin suka yi a Borno, an gano cewa sun bukaci dala 500,000 a matsayin kudin fansarsu.

A wani bidiyo da mayakan suka saki a ranar Laraba, an ga yadda aka kashesu, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Idan za mu tuna, an sace ma'aikatan ne a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Monguno a watan da ya gabata.

Sun sako bidiyon ma'aikatan inda suke rokon gwamnatin tarayya tare da kungiyoyinsu da su taimaka wurin bada kudin fansarsu.

Bidiyon rokon ya bayyana ne a cikin watan da ya gabata mai tsawon minti biyu. 'Yan ta'addan ne suka saki bidiyon da ke nuna ma'aikatan tare da mai gadin.

Da duminsa: Boko Haram ta saki bidiyon kisan gilla da suka yi wa ma'aikatan SEMA da mai gadi
Da duminsa: Boko Haram ta saki bidiyon kisan gilla da suka yi wa ma'aikatan SEMA da mai gadi. Hoto daga HumAngle
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan siyasa 5 da 'ciwonsu ya tashi' a yayin da ake bincikarsu a kan rashawa (Hotuna)

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta ce dakarun sojin saman Rundunar Operation Hadarin Daji sun ragargaza sansanin 'yan bindiga a samamen da ta kai ta jiragen yaki a dajin Kagara na jihar Zamfara.

Kamar yadda Shugaban fannin yada labarai na rundunar, John Enenche ya sanar a ranar Laraba a Abuja, dakarun sun kai samamen ne a ranar 20 ga watan Yulin 2020.

Enenche ya ce sun kai samamen ne bayan rahotannin sirri da suka samu na 'yan bindigar da ke dajin tare da dabbobin da suka sace a wani sassa na dajin.

Ya ce an tabbatar da rahotannin sirrin bayan leken asirin da aka yi ta jiragen yaki. Hakan ne yasa aka ragargaza maboyar da ruwan bama-bamai.

Kamar yadda yace, jiragen rundunar sojin saman sun isa wurin inda suka dinga ruwan bama-bamai da ya kai ga kisan wasu daga cikin 'yan bindigar.

"Wasu daga cikin 'yan bindigar da suka yi yunkurin tserewa ta hanyar shigewa cikin dabbobin, duk an damke su."

Shugaban dakarun sojin sama, Sadique Abubakar, ya jinjinawa rundunar a kan kwarewar da suka bayyana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel