An bawa Sarkin Shinkafi wa'addin awa 24 ya kwace sarautar da ya bawa Fani-Kayode

An bawa Sarkin Shinkafi wa'addin awa 24 ya kwace sarautar da ya bawa Fani-Kayode

An bawa Sarkin Shinkafi, Alhaji Muhammad Makwashe waadin awa 24 ya janye sarautar gargajiyar da ya bawa tsohon ministan Sufurin Jiragen Sama Femi Fani-Kayode.

Hakan na zuwa ne bayan masu rike da sarauta biyu a masarautar sun yi murabus domin nuna rashin amincewarsu da nada Fani Kayode a matsayin Sadaukin Shinkafi.

Masu rike da saurautun gargajiyan biyu da suka yi murabus sune Dr Sulaiman Shuaibu, Sarkin ‘Shanun Shinkafi’ da Dr Tijjani Salihu Shinkafi mai sarautar ‘Sarkin Marayun Shinkafi’.

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a Kaduna, Dr Suleiman Shuaibu Shinkafi da ya yi magana a madadin kungiyar Shinkafi Concerned Citizens ya yi kira ga sarkin ya janye wannan nadin sarautan da ya yi.

Ya kuma yi kira ga sauran masu rike da sarautun gargajiya a masarautar Shinkafi suma suyi murabus domin Fani Kayode bai cancanci sarautar da aka nada masa ba.

An bawa Sarkin Shinkafi wa'adi ya kwace sarautar da ya bawa Fani-Kayode
Femi Fani-Kayode. Hoto daga Guardian
Asali: UGC

"Mu yan asalin Shinkafi ba mu amince da sarautar Sadaukin Shinkafi da aka bawa Femi Fani Kayode ba a jihar Zamfara saboda bai cancanta a bashi wannan sarautar ba.

"Wannan mutum ne da aka sani ya saba cin mutunci da zagin shugabanin mu da iyaye da kakkanin mu na yankin arewa.

DUBA WANNAN: Budurwa ta bindige saurayinta saboda ya ki biye mata suyi cacar baki

"A kan haka, na yi ajiye sarautar da sarki ya bani na Sarkin Shanun Shinkafi kuma abokin aiki na, Dr Tijjani Salihu na Jamiar Danfodio shima ya ajiye sarautarsa ta Sarkin Marayun Shinkafi," in ji shi.

Shuaibu ya ce kungiyar za ta garzaya kotu muddin ba a janye sarautar gargajiyar da aka bawa Fani Kayode ba.

"Muna kuma sa ran wasu masu sarautar gargajiya shida za su ajiye sarautarsu a yau," a cewarsa.

Ya cigaba da cewa mambobin kungiyar Shinkafi Concerned Citizens mafi yawancinsu masu rike da sarautun gargajiya ne a masarautar kuma ba su gamsu da matakin da sarkin ya dauka ba.

"Wannan matakin da aka dauka bai dace ba kuma ba za mu amince ba, ba a tuntube mu ba saboda haka ba za ta sabu ba.

"Bayan awa 24 idan ba a janye sarautar ba, Sarki ya shirya fuskantar doka kuma shima zai yi murabus.

"Za mu gudanar da zanga zanga a kan wannan nadin, Kayode bai cancanci a bashi wata sarauta ba a arewa kuma ba za mu amince ba a bashi," in ji shi.

A dai karshem makon da ta gabata ne Masarautar Shinkafi ta nada Fani Kayode sarautar “Sadaukin Shinkafi”.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun sarkin, Alh Muhammad Makwashe da aka raba wa manema labarai a Gusau a ranar Litinin, sarkin ya ce ya bawa tsohon ministan sarautar ne saboda gudunmuwar da ya bawa masarautar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel