Shugaba a DSS ya shararawa ma'aikacin filin jirgin sama mari – FAAN

Shugaba a DSS ya shararawa ma'aikacin filin jirgin sama mari – FAAN

An zargi shugaban Hukumar Yan Sandan Farar Hula, SSS, na filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, NAIA, Safiyanu Abba da marin wata ma'aikaci a filin tashin jiragen.

A ranar Laraba, Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama na Tarayya, FAAN, ta ce Mr Abba ya saba dokokin tsaro kuma ya doki wani jami'an hukumar da ta nemi ta yi masa gyara a ranar Jumaa.

FAAN ta ce shugaban na SSS ya hana ma'aikatan da ke filin jiragen saman su gudanar da aikinsu na bincikar duk wani fasinja da ya sauka ko zai shiga jirgi.

Shugaba a DSS ya shararawa ma'aikaciyar filin jirgi mari – FAAN
Shugaba a DSS ya shararawa ma'aikaciyar filin jirgi mari – FAAN
Asali: UGC

Hukumar ta FAAN ta sanar da hakan ne ta shafin ta na Twitter mai lakabin @FAAN_Official

"Muna bakin cikin sanar da cewa Mr Safiyanu Abba, Shugaban DSS a NAIA da gangan ya hana maaikatan filin tashin jirage yin aikinsu, ya kuma mari wani maaikaci da ke bakin aikinsa saboda ya tunatar da shi dokar da ya ke karyawa.

"Wannan abin ya faru ne a ranar 17 ga watan Yuli misalin karfe 3:25 na yamma. Ya saba dokar tsaro yayinda ya hana a bincika wani bako da ya wuce cikin naurar bincika mutane kuma naurar ta nuna yana dauke da karfe a jikinsa," kamar yadda sanarwar ta ce.

DUBA WANNAN: Budurwa ta bindige saurayinta saboda ya ki biye mata suyi cacar baki

FAAN ta yi Allah wadai da wannan abin inda ta ce hakan ya saba dokokin aiki tare da kawo cikas ga ayyukan ta a filin tashi da saukan jiragen.

Sai dai Mai magana da yawun DSS, Peter Afunaya ya musanta wannan zargin.

Da ya ke martani a kan rahoton a yayin da Premium Times ta tuntube shi a ranar Laraba. Ya ce suna da alaka mai kyau da hukumar FAAN.

"Wannan ba gaskiya bane. Maaikatan DSS suna da halaye masu kyau saboda haka babu yadda za ayi suyi fada ko su mari jamian wata hukuma da suke aiki tare. FAAN da DSS suna bawa alakarsu muhimmanci domin samun nasara a wurin aiki."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel