Hotuna da bidiyo: Yadda sojin sama suka ragargaza 'yan bindiga a dajin Kagara
Hedkwatar tsaro ta ce dakarun sojin saman Rundunar Operation Hadarin Daji sun ragargaza sansanin 'yan bindiga a samamen da ta kai ta jiragen yaki a dajin Kagara na jihar Zamfara.
Kamar yadda Shugaban fannin yada labarai na rundunar, John Enenche ya sanar a ranar Laraba a Abuja, dakarun sun kai samamen ne a ranar 20 ga watan Yulin 2020.

Asali: Twitter
Enenche ya ce sun kai samamen ne bayan rahotannin sirri da suka samu na 'yan bindigar da ke dajin tare da dabbobin da suka sace a wani sassa na dajin.
Ya ce an tabbatar da rahotannin sirrin bayan leken asirin da aka yi ta jiragen yaki. Hakan ne yasa aka ragargaza maboyar da ruwan bama-bamai.

Asali: Twitter
Kamar yadda yace, jiragen rundunar sojin saman sun isa wurin inda suka dinga ruwan bama-bamai da ya kai ga kisan wasu daga cikin 'yan bindigar.
"Wasu daga cikin 'yan bindigar da suka yi yunkurin tserewa ta hanyar shigewa cikin dabbobin, duk an damke su."

Asali: Twitter
Shugaban dakarun sojin sama, Sadique Abubakar, ya jinjinawa rundunar a kan kwarewar da suka bayyana.
KU KARANTA: 'Yan siyasa 5 da 'ciwonsu ya tashi' a yayin da ake bincikarsu a kan rashawa (Hotuna)
Ya yi kira garesu da su ci gaba da kokarin da suke yi ta hanyar bada goyon baya ga dakarun sojin kasan don tabbatar da kawo karshen 'yan bindiga.
Hakan kuwa shine cikar umarnin shugaban ma'aikatan tsaro na dawo da zaman lafiya yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya ta kasar nan.

Asali: Twitter
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng