'Yan sanda a Italy sun kama 'yan Najeriya 15 da ke kungiyar asiri

'Yan sanda a Italy sun kama 'yan Najeriya 15 da ke kungiyar asiri

An kama mutanen da ake zargin ne a wata atisaye da aka yi mai suna “Pesha” da aka kammala a ranar Talata.

Sanarwar da yan sandan suka fitar ta ce yan kungiyar asirin suna yi wa yan mata barazana suna tilasta musu yin karuwanci, safarar kwayoyi, almundahanar kudi da wasu laifukan.

The Cable ta ruwaito cewa wadanda aka kama din yan kungiyar asiri ta “Eiye” ne da ta samo asali a Najeriya kuma ta ke da mambobi a wasu kasashe.

"Mutane 15 da L’Aquila District Anti-Mafia Directorate ta bayar da umurnin tsare su 'yan Najeriya ne," in ji sanarwar.

"Dukkan wadanda aka kama yan kungiyar “Pesha” ne da ke da mambobi a yankin Adriatic da Teramo zuwa Ancona.

'Yan sanda a Italy sun kama 'yan Najeriya 15 da ke kungiyar asiri
'Yan sanda a Italy sun kama 'yan Najeriya 15 da ke kungiyar asiri. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Budurwa ta bindige saurayinta saboda ya ki biye mata suyi cacar baki

"Laifufukan da yan kungiyar asirin suka aikata suna da yawa: Almundahanar kudade; Safarar yan mata domin karuwanci a Bonifica del Tronto road da cin mutuncinsu; safarar kwayoyi; Fada da wasu yan kungiyoyin asirin da mutanen kasa."

'Yan sandan sun ce daya daga cikin mamban kugiyar asirin ne ya tona su sakamakon hukunta shi da aka yi saboda ya saba wasu dokokin kungiyar.

Rundunar yan sandan ta ce jami'anta sun kai sumame mabuyar yan kungiyar inda suka yi nasarar kama 15 daga cikinsu.

Ta ce akwai wasu mambobi hudu da ake nema har yanzu amma wadanda aka kama suna hedkwatan 'yan sanda da ke Teramo kuma za a gurfanar da su gaban kuliya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel