Gwamnati kadai ba za ta iya inganta gine-ginen kananan makarantu ba - Nwajiuba

Gwamnati kadai ba za ta iya inganta gine-ginen kananan makarantu ba - Nwajiuba

- Karamin Ministan Ilimi ya kai wa Sarkin Kano ziyara a ranar Talata

- Chukwuemeka Nwajiuba ya bayyana damuwa kan yadda lalacewar da gine-ginen kananan makarantu suka yi ta kai munzali na intaha

- Ministan yace gwamnati kadai ba za ta iya farfado da gine-ginen makarantun ba

A ranar Talata ne Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, ya kai wa Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ziyara har fadarsa da ke kwaryar birnin Dabo.

Nwajiuba ya bayyana damuwa matuka dangane da yanayi na koma bayan kayan gine-ginen kananan makarantu a fadin kasar, lamarin da ya ce abin kunya ne.

Sai dai ministan ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta iya magance wannan matsala ba ita kadai kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Karamin Ministan Ilimi; Chukwemeka Nwajiuba
Karamin Ministan Ilimi; Chukwemeka Nwajiuba
Asali: UGC

Mista Nwajiuba ya bayyana hakan ne yayin gabatar da wata kyauta ga Sarkin Kano ta Alamar Sarauta ta Kyautata Makomar Yaran Najeriya mai suna Royal Icon of Hope for Nigerian Children.

Ya ce don haka akwai bukatar masu hali da sauran rassan masu zaman kansu su shiga lamarin domin kawo karshen wannan kalubale da makomar ilimin yara ke fuskanta.

Ministan wanda hadiminsa na musamman Injinya Adewale Adenaike ya wakilta, ya ce domin farfado da gine-ginen makarantun cikin gaggawa, an kaddamar da wani shiri na musamman karkashin Asusun Gidauniyar Naija.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Gwamnatin Jihar Kano ta soke bukukuwar babban sallah da aka saba yi duk shekara a jihar a bana.

KARANTA KUMA: Ondo 2020: Yadda Akeredolu ya lashe tikitin takara na jam'iyyar APC

Gwamnatin ta ce ta dauki wannan matakin ne domin cigaba da dakile bazuwar annobar COVID-19 duk da cewa an sassauta dokar zirga zirga a tsakanin jihohi.

Kwamishinan labarai na jihar, Mallam Muhammad Garba yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a ranar Laraba ya ce an dauki matakin ne yayin taron Majalisar Zartarwa na Jihar da aka yi ranar Talata.

Ya ce duk da cewa an bayar da izinin yin sallar idi a jihar, za a gudanar da sallar ne bisa ka'idodin da hukumomin lafiya suka shar'anta na bayar da tazara da saka takunkumin rufe fuska da sauransu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel