Wutar lantarki ta haddasa gobara a Ofishin NTA na Ilorin, dakuna 3 da dakin taro sun kone

Wutar lantarki ta haddasa gobara a Ofishin NTA na Ilorin, dakuna 3 da dakin taro sun kone

- Gobara ta tashi a ginin NTA na Ilorin jihar Kwara a daren ranar Talata

- Ana kyautata zaton wutar lantarki ce ta haddasa gobarar, wacce ta lakume dakuna uku

- Gwamnan jihar AbdulRahman AbdulRazaq ya jajantawa hukumar gudanarwar NTA kan lamarin

Rahotanni sun bayyana cewa gobara ta tashi a daren ranar Talata a ginin ofishin talabijin na NTA, da ke Ilorin, jihar Kwara.

Gobarar, wacce ake da yakinin wutar lantarki ce ta haddasa ta, ta fara ne da misalin karfe 11:25 na daren kuma ta shafi dakuna uku da dakin taro.

Mai magana da yawun hukumar 'yan kwana kwana na jihar Kwara Hassan Adekunle ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar The Nation.

Ya ce: "Daga cikin ofisoshi 28 na cikin ginin, ofisoshi uku ne kawai suka kone da kuma dakin taro."

Adekunle ya ce 'yan kwana kwana "sun isa ginin da misalin karfe 11:29 mintuna hudu bayan da aka rufe watsa labarai na wannan rana.

"Duk da cewa lokacin da suka isa wajen, wutar na ci sosai kuma har ta mamaye wurare da dama a cikin ginin

"Yan kwana kwanan sun samu nasarar kashe wutar ta hanyar amfani da kayan aikinsu na zamani."

KARANTA WANNAN: Yanzu: Majalisar dattijai ta ba Buhari nan da Satumba ya gabatar da kasafin 2021

Wutar lantarki ta haddasa gobara a Ofishin NTA na Ilorin, dakuna 3 da dakin taro sun kone
Wutar lantarki ta haddasa gobara a Ofishin NTA na Ilorin, dakuna 3 da dakin taro sun kone
Asali: Twitter

Ya bukaci "daukacin al'umma (musamman masu aiki) da su kasance suna kashe dukkanin kayayyakin wutar lantarki bayan tashi daga aiki."

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar ya jajantawa hukumar gudanar NTA kan faruwar wannan lamari.

A cikin wata sanarwa daga bakin mai magana da yawunsa, Rafiu Ajakaye, gwamnan ya ce ya isa ginin gidan talabijin din da misalin karfe daya na ranar Laraba.

Ya ce lallai da gobarar ta lashe dukkanin ginin amma sakamakon hadin karfi tsakanin 'yan kwana kwana na gwamnatin tarayya da na jiha, an shawo kanta.

Ajakaye yace: "Muna jajantawa NTA akan wannan lamari. Amma abun farin cikin shine ba a yi asarar rayuka ba.

"Haka zalika kawo agajin gaggawa da 'yan kwana kwana suka yi ya taimaka ainun wajen dakile yaduwar wutar."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel