Gwamnatin Kano ta soke bukukuwar babbar Sallah a Kano

Gwamnatin Kano ta soke bukukuwar babbar Sallah a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta soke bukukuwar babban sallah da aka saba yi duk shekara a jihar a bana kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta ce ta dauki wannan matakin ne domin cigaba da dakile yaduwar annobar COVID-19 duba da cewa an sassauta dokar zirga zirga a jihohi da dama har da Kano.

Kwamishinan labarai na jihar, Mallam Muhammad Garba yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a ranar Laraba ya ce an dauki matakin ne yayin taron Majalisar Zartarwa na Jihar da aka yi ranar Talata.

Gwamnatin Kano ta soke bukukuwar babbar Sallah a Kano
Gwamnatin Kano ta soke bukukuwar babbar Sallah a Kano. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Budurwa ta bindige saurayinta saboda ya ki biye mata suyi cacar baki

Ya ce duk da cewa an bayar da izinin yin sallar idi a jihar, za a gudanar da sallar ne bisa kaidojin da hukumomin lafiya suka bayar na tazara da saka takunkumin fuska da sauransu.

Garba ya kara da cewa dukkan sarakuna biyar na jihar za su tafi masalatan Idi a cikin motocinsu sannan babu ziyara zuwa gidan Shettima, Hawan Daushe, Hawan Nasarawa da sauran bukukuwa.

Kazalika, gwamnati za ta taimaka wurin samar da kayayyakin tsare lafiya kamar takunkumin fuska, sinadarin wanke hannu, hand sanitizer, kuma za ta tabbatar mutane sun bayar da tazara a filayen sallar Idi.

A wani labarin, Gwamnan Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar shima ya soke bukukuwan babbar Sallar Layya a jihar da kuma dakatar da sarakuna biyar masu daraja na jihar daga jagorantar duk wani hawan Sallah ko hawan daushe a babbar Sallar wannan shekarar.

Gwamnan ya bayar da wannan umurnin ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.

A tattaunawar, ya ce wannan umurnin na daga cikin yunkurin gwamnatin jihar na ci gaba da yaki don dakile yaduwar cutar COVID-19.

Ya bayyana cewa, jihar a yanzu ta samu gagarumar nasara ta wannan fuskar, kasancewar bata samu bullar cutar ba kusan kwanaki 30 yanzu.

Gwamnan jihar ya bayyana cewa: "duk da irin wannan nasarar, dole ne jihar ta bi duk wasu matakai na dakile bullar cutar da kuma daukar matakan kariya na dakile yaduwarta."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel