Budurwa ta bindige saurayinta saboda ya ki biye mata suyi cacar baki
Wata mata mai shekara 29 mai suna Jenalisha Lawrence ta tsere daga gida bayan ta harbi saurayinta da bindiga domin ya ki biye mata suyi cacar baki.
A halin yanzu jami'an 'yan sanda na neman ta kuma suna rokon mutane su taimaka musu da bayanai da zai taimaka a gano inda ta shi.
Matar ta tsere ne bayan ta harbi saurayinta mai shekara 34 ta bar shi a gefen titi cikin mawuyacin hali shi kadai.
Jenalisha ta ja motar ta ta tsere zuwa Dallas, Texas a Amurka inda dama nan ne asalin garin su.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Wani ya kashe kansa a harabar ofishin hukuma saboda tarar N215,000
Tuni dai an bayar da izinin a kamo ta bayan an tuhume ta da yunkurin kisar kai. An kuma saka laada a kan ta na Dallar Amurka 150,000.
Harbin ya faru ne misalin karfe 7.30 na safe a block 400 na Grigsby Street a unguwar Caddo Heights da ke Shreveport.
'Yan sanda a Shreveport sun ce an kira su gidan ne a kan cewa an ji karar harbin bindiga kuma da suka isa sai suka tarar da mutumin mai shekara 34 a gefen titi da raunin bindiga a jikinsa.
An kai shi asibitin Ochsner LSU Health da ke Shreveport da munanan rauni a jikinsa kuma har yanzu yana cikin mummunan hali a cewar KXAN.
Masu bincike sun isa wurin da abin ya faru kuma bayan yi wa wadanda abin ya faru a idonsu tambayoyi sun ce Lawrence ta harbi mutumin ne domin ya ki biye mata suyi cacar baki.
Bayan harbinsa ta tsere a cikin motar kirar Honda launin kore da wani abu mai kamar na hada abin fashewa a kujerar motar na gaba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng