Da duminsa: Gwamna a arewa ya dakatar da basarake a jiharsa

Da duminsa: Gwamna a arewa ya dakatar da basarake a jiharsa

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya dakatar da hakimin Mbatser/Mbamusa da ke karamar hukumar Konsisha ta jihar yayin da ya dage dakatar da wasu hakimai uku na yankin Katsina-Ala.

Dakatarwar ta shafi basarake Zaki Mbanongun Gbakera, sakamakon sabon rikici tsakanin jama'arsa na Konshisha da na yankin Igede da ke karamar hukumar Oju.

Ortom ya ce sun yanke wannan hukuncin ne bayan taron da suka yi da jami'an tsaro a gidan gwamnatin jihar da ke Makurdi.

"An yanke shawarar dakatar da hakimin Mbatser/Mbamusa da ke karamar hukumar Konsisha ta jihar, Zaki Mbanongun Gbakera saboda sake rikicewar al'amarin.

"An bukaci Tor Tiv da ya nada mukaddashin hakimin tare da kwamitin bincike a kan basaraken.

"Taron ya yanke hukuncin cewa Bonta da Ukpute na Konshisha da Oju sun tabbatar da cewa zaman lafiya ya dawo yankin," yace.

Ya kara da cewa, taron ya yanke hukuncin cewa a gaggauta saka iyaka tsakanin wasu kananan hukumomi biyu don gujewa ci gaban rikici a yankin.

Da duminsa: Gwamna a arewa ya dakatar da basarake a jiharsa
Da duminsa: Gwamna a arewa ya dakatar da basarake a jiharsa. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Ministan Buhari ya bayyana gaban kwamitin bincike

A kan rikicin Katsina-Ala, ya ce majalisar jami'an tsaro ta jihar ta dage dakatarwar da ta yi wa sarakunan gargajiya uku da ke yankin Sankera. Sune: Mue Ter Chongo, Mue Term Ipusu da Tyoor Luke Atomigba, hakimai a Mbacher da ke Shitile.

An dakatar da su a ranar 19 ga watan Augustan 2019 na tsawon watanni shida a kan karantsaye ga dokokin masarautun gargajiya da majalisar sarakunan jihar Binuwai.

Hakazalika, taron ya yanke shawarar cewa, kwamitin da aka kafa don duba rikicin yankin Sankera, cewa For Sankera zai koma Katsina-Ala da gaggawa kafin karewar watan Yulin 2020.

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun kashe dagajin kauyen Gora Gan da ke karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna da wasu mutane tara.

Wannan na zuwa na kimanin awa 24 bayan kashe wasu matasa 21 yayin bikin daurin aure a kauyen Kukum Daji da ke karamar hukumar Kaura.

The Nation ta ruwaito cewa har da wani yaro mai shekara shida cikin wadanda aka kashe a harin na baya bayan nan tare da jikkata wasu mutane da dama.

Wani wanda abin ya faru a idonsa ya ce yan bindiga kimanin su 20 ne suka kai farmaki kauyen misalin karfe 7 na yamma a ranar Litinin suka fara harbe harbe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel