Mutane 5 makusanta da shugaba Buhari ya rasa a wannan shekarar

Mutane 5 makusanta da shugaba Buhari ya rasa a wannan shekarar

A cikin shekarar nan, shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya rasa mutane makusanta. Daga cikinsu kuwa akwai wanda ba sai an fada ba, mutuwar ta girgiza shi.

Malam Isma'ila Isa-Funtua

Babu shakka rasuwar Malam Isma'ila Isa Funtua a ranar Litinin ta matukar girgiza shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Alamu sun nuna cewa shugaban kasar ya girgiza ganin na hannun damansa, Abba Kyari, bai dade da rasuwa ba.

A yayin ta'aziyyar marigayin, Buhari ya ce mutuwarsa ta samar da babban gibi.

A sanarwar da Garba Shehu ya fitar, ya sanar da cewa "marigayin mutum ne na Kowa kuma ana matukar girmama shi."

Isma'ila Funtua na cikin manyan masu tasiri a gwamnatin Buhari.

Buhari ya ce, rasuwar matashin ministan a jamhuriya ta biyu zai haifar da babban gibi saboda taimakon da yake samu ta wurinsa a tafiyarsa ta siyasa.

Mutane 5 makusanta da shugaba Buhari ya rasa a wannan shekarar
Mutane 5 makusanta da shugaba Buhari ya rasa a wannan shekarar. Hoto daga ThisDay
Asali: Twitter

Rasuwar Ibrahim Dauda da Muntari Dauda

Wadannan makusantan shugaba Buhari ne da suka rasu a cikin wannan shekarar.

Ibrahim Dauda ya rasu ranar 30 ga watan Mayu inda kwanaki kadan Muntari Dauda yace ga garinku.

KU KARANTA: Da duminsa: Wani ministan Buhari ya killace kansa

Rasuwar Hajiya Halima Dauda

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasa Hajiya Halima Dauda, mahaifiyar Sabiu Tunde, daya daga cikin mataimakinsa na musamman.

A sakon ta'aziyyar shugaban kasa, ya ce wannan rasuwar ta taba iyalansu da daukacin al'ummar Daura.

Rasuwar Abba Kyari

A cikin watan Mayu, shugaban fadar ma'aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abba Kyari, ya rasu. Buhari ya kwatanta Kyari da babban amininsa kuma mai matukar kishin kasa.

A ta'aziyyar mai taken 'Zuwa ga Abokin Abba Kyari' shugaban kasar ya ce marigayin amininsa ne na tsawon shekaru 42 da suka shude, wanda daga baya ya zama shugaban ma'aikatan fadarsa.

Malam Abba Kyari ya rasu yana da shekaru 67 bayan fama da yayi da cutar korona.

Buhari ya ce ya fara haduwa da Kyari tun yana saurayi mai shekaru 20.

"Bai taba kasa a guiwa ba wurin sadaukar da kansa ga ci gaban kowannenmu ba.

"Abba Kyari mutum ne na kwarai wanda ya fi mu," in ji Buhari.

Mutane 5 makusanta da shugaba Buhari ya rasa a wannan shekarar
Mutane 5 makusanta da shugaba Buhari ya rasa a wannan shekarar. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel