Ma'aikata 774,000: Sanata ya yiwa Keyamo barazana da shiga gidan yari

Ma'aikata 774,000: Sanata ya yiwa Keyamo barazana da shiga gidan yari

Bala Na'Allah, Sanatan da ke wakiltar Kebbi ta Kudu, ya ce Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da samar da aikin yi, yana fuskantar hadarin shiga gidan yari kan shirin daukan ma'aikata 774,000.

Sanata Na'Allah yace Mista Keyamo ya tsame hannunsa daga lamarin domin kuwa sabawa kundin tsarin mulkin kasar nan zai iya jefa shi a gidan kaso.

Da yake ba da gudummawa ga kudirin da Opeyemi Bamidele, Sanata mai wakiltar Ekiti ta tsakiya ya gabatar a ranar Talata, Na'Allah ya ce rawar da Keyamo zai taka a daukar ma'aikatan kawai sa ido ne.

A baya bayan nan ne cikin watan Yuli, wasu 'yan majalisar dattawa suka yi musayar yawu da Ministan kan batun daukan ma'aikatan yayin da ya bayyana a zauren majalisar.

Ministan kwadago da samar da aikin yi; Festus Keyamo
Hoto daga Pulse.ng
Ministan kwadago da samar da aikin yi; Festus Keyamo Hoto daga Pulse.ng
Asali: Twitter

Majalisar ta ce ministan ba ya da 'ruwa ko tsaki' kan batun aiwatar da shirin wanda a cewarta aiki ne da ya kebanci Hukumar samar da ayyuka ta NDE.

Majalisar ta nemi ministan ya tsaya a matsayinsa na mai tabbatar da kula a kan Hukumar NDE, wadda ke karkashin ma'aikatarsa.

A yayin da majalisar take tuhumar Keyamo da yi wa shirin daukan ma'aikatan shisshigi ga Hukumar NDE, shi kuma ministan ya ce 'yan majalisar na kokarin yi wa lamarin hawan kawara saboda son zuciya.

KARANTA KUMA: Bidiyo: Sojoji sun lakaɗawa wani mutum duka a Abiya

‘Yan majalisar dokokin tarayyar sun zargi Keyamo da kwace shirin daukar ma’aikatan daga hukumar NDE wacce ta samu naira biliyan 52 domin aiwatar da shirin.

Da yake jawabi kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, Sanata Na'Allah ya ce ministan ba ya da hurumin aiwatar da hakan domin kuwa kundin tsarin mulkin kasa bai ba shi wannan dama ba.

Haka zalika, shugaban majalisar dattawan Sanata Ahmed Lawan, ya ce majalisar ba za ta gushe ba kan cewa Hukumar NDE ce ke da ruwa da tsaki a shirin daukan ma'aikatan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel