Neman sauke hafsoshin tsaro: Buhari ya 'watsa wa ƴan majalisa kasa a ido'

Neman sauke hafsoshin tsaro: Buhari ya 'watsa wa ƴan majalisa kasa a ido'

Fadar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a ranar Talata ta ce shugaban kasar ne kawai ke da ikon sauke shugabanin hukumomin tsaron kasar da nada sabbi.

Ta yi wannan jawabi ne a matsayin martani ga kiran da Majalisar Dattawar Kasar ta yi a ranar Talatar ne neman shugabanin hukumomin tsaron su yi murabus ko kuma a tsige su saboda tarbarewar tsaro.

Cikin dalilin da ya sanya majalisar dattawar neman shugabanin tsaron su yi murabus har da rahoton ajiye aiki da aka ce wasu sojoji fiye da dari biyu sunyi saboda sun gaji da yadda ake kashe su yayin yaki da taadanci.

Fadar shugaban kasa ta yi martani kan bukatar da Majalisa ta yi na shugabannin tsaro su ajiye aikinsu
Shugabannin tsaro. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Majalisar ta cimma maytsayar neman shugabanin tsaron su yi murabus ne sakamakon kudin da Shugaban kwamitin majalisar a kan Sojoji, Sanata Mohammed Ali Ndume (Borno South)ya gabatar.

DUBA WANNAN: Wani ya kashe kansa a harabar ofishin hukuma saboda tarar N215,000

Sai dai fadar shugaban kasar cikin wata gajeruwar sako mai taken, "Matsayar fadar shugaban kasa a kan matakin da Majalisar Dattawa da dauka" ta ce Buhari ne kadai ke da ikon nada shugabanin hukumomin tsaro ko sallamarsu.

Sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar da shafinta na Twitter @NGRPresident ya ce: "Majalisar Dattijai a ranar Talata ta bukaci Shugabannin hukumomin tsaro su yi murabus ko kuma a sauke su saboda kallubalen tsaro da ke adabar kasar.

"Fadar shugaban kasa ta sauke shugabanin tsaro aikin Shugaban kasa ne kuma Shugaba Muhammadu Buhari a matsayinsa na shugaban hafsoshin Najeriya zai yi abinda yafi dacewa da Najeriya a kowanne lokaci."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel