Mudassir & Brothers ya dauki matasa 400 aiki a Kano

Mudassir & Brothers ya dauki matasa 400 aiki a Kano

Mudassir and Brothers, shahararren kamfanin sayar da kayayyakin more rayuwa a birnin Kanon Dabo, ya dauki matasa 400 aiki 'yan asalin jihar a wani sabon shago da ya buɗe.

Shugaban kamfanin da ya kasance matashin dan kasuwa kuma Attajiri, Mudassir Abubakar, shi ne ya bayyana hakan yayin buɗe katafaren shagon nasa a ranar Asabar.

A cewarsa, makasudin kafa irin wannan cibiya ta kasuwanci shi ne samar da aikin yi ga matasan jihar tare da lura da cewa cibiyar hada-hadar bunkasa samuwar kudaden shiga ce ga gwamnatin Kano.

Mudassir ya kuma sanar da cewa ya sadaukar da cibiya ta kasuwanci wacce ita ce ta 13 da ya kafa a kasar, ga mahaifinsa wanda marigayi ne.

A nata jawaban, Mahaifiyar Mudassir, Hajiya Binta Muhammad, wadda ta jagoranci bikin buɗe sabon shagon, ta yi godiya ga Mahaliccinta wanda Ya azurta ta da lafiya har ta kai ga ganin wannan rana.

Sabon kantin Mudassir & Brothers
Hakkin mallakar hoto; Daily Nigerian
Sabon kantin Mudassir & Brothers Hakkin mallakar hoto; Daily Nigerian
Asali: Twitter

Yayin yi wa daukacin al'ummar jihar Kano godiya ta addu'o'i da kuma goyon bayan ɗanta da suke yi, Hajiya Binta ta kuma yabawa gwamnatin Kano da ta samar da kyakkyawan yanayi na gudanar da harkokin kasuwanci a jihar.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, sabon shagon da aka buɗe yana nan a kan titin Igbo daura da kasuwar Sabon Gari cike makil da kayayyaki kamar sutura, kayan daki da sauransu.

A baya bayan ne gwamnatin Kano ta musanta zargin da ake yi mata da cewa ta cefanar da Otal din Daula ga mamallakin kamfanin Mudassir and Brothers.

Gidan Rediyon Freedom ya ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne aka yi ta yada jita-jitar cewa gwamnatin Kano ta sayarwa da hamshakin dan kasuwar daɗaɗɗen Otal ɗin domin ya gina kanti na komai da ruwanka a wurin.

KARANTA KUMA: An yi bikin ƙara wa 'yan sanda 10 girma a Abuja

Gwamnatin Kano ta ce maganar sayar da Otal din bata taso ba, amma ta fara kulla yarjejeniya da Alhaji Mudassir domin bunkasa wannan wuri da nufin inganta rayuwar al'ummar jihar.

Kwamishinan kudi na jihar Alhaji Shehu Na'Allah Kura, shi ne ya bayyana hakan da cewa, gwamnatin ta yi hakan ne sakamakon mummunan yanayi da Otal din yake ciki a yanzu.

Alhaji Na'Allah ya ce gwamnatocin baya sun yi watsi da Otal din a yanzu lalacewarsa ta kai ga har ya zama barazana ga al'umma.

Kamar yadda kwamishinan ya bayyana, wannan shine dalilin da ya sanya gwamnatin jihar ta shiga cigiyar wanda zai farfado da wannan wuri domin bunkasa ci gaban al'umma da kuma jihar baki daya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel