'Yar shekara 107 ta warke daga cutar korona a Saudiya

'Yar shekara 107 ta warke daga cutar korona a Saudiya

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, wata tsohuwa 'yar shekaru 107 ta warke daga cutar korona bayan an yi mata magani a wani asibitin Jeddah da ke kasar Saudiya.

A cewar Dakta Khaled Al-Ghamdi, babban darektan Asibitin mai suna East Jeddah Hospital, ya ce matar ta yi fama da matsaloli na numfashi.

Ya bayar da shaidar yadda ta yi jinya a sashen ba da kulawar gaggawa na asibitin inda tawagar kwararrun likitoci karkashin jagorancin Dakta Ruba Hindi da kuma Badour Al-Otaibi suka sa ido har ta warke.

Ya ce "an gano tsohuwar ta harbu da cutar korona wadda kuma ta haddasa mata kamuwa da cutar sanyi (Pneumonia) da kuma karancin numfashi."

"Hakan ya sanya dole aka sa mata na'urar da ke taimaka wa numfashi har na tsawon kwanaki hudu."

Asibitin na East Jeddah General Hospital
Hoto daga Saudi Gazette
Asibitin na East Jeddah General Hospital Hoto daga Saudi Gazette
Asali: UGC

"Daga bisani an mayar da ita sashen bayar da kulawa ta musamman inda aka ba ta duk wani magani da zai warkar mata da cutar bisa la'akari da ka'idodin da Ma'aikatar Lafiya ta shar'anta."

"Bayan ta shafe tsawon mako guda ta na jinya, tsohuwar ta fara samun lafiya da har ta kai an dauke ta daga kan na'urar mai taimakon numfashi."

Al-Ghamdi ya kara da cewa, a yanzu haka an sallami dattijuwar daga asibitin bayan ta samu cikakkiyar lafiya.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Sarki Salman Bin Abdul'aziz na kasar Saudiya, ya na kwance a wani asibiti sakamakon larura da ya samu a mafitsararsa.

Rahotannin da su ke fito daga gidajen jaridun kasar a ranar Litinin, sun tabbatar da cewa an kwantar da sarkin mai shekaru 84 a asibiti.

SPA, Kamfanin dillacin labarai na kasar Saudiya ya bayyana cewa an dai kwantar da Salman Bin Abdul'aziz ne a wani asibiti da ke Riyadh, babban birnin kasar.

KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da 'yan fashi 43 a Adamawa

Bayan rahotannin cewa Sarki Salman ya na fama da kumburi a mafitsararsa, babu wani labari da aka samu game da halin shugaban.

Yanzu haka ana yi wa Sarkin na Saudiyya, kuma mai kula da masallatan musulunci masu tsarki da ke biranen Makkah da Madina gwaje-gwaje a asibiti.

Dattijon Sarkin ya yi shekaru biyar ya na mulki, amma ana ganin babban ‘dansa kuma yarima mai jiran gado watau Mohammed ‘dan Salman ya ke jan ragamar kasar.

Sakamakon rashin lafiyar da ta kama Sarkin, Firayim Ministan kasar Iraki, Mustafa al-Kadhimi, ya dakatar da ziyarar da ya yi niyyar kai wa zuwa kasar Saudi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel